Zaben 2023: Gwamna Sanwo Olu Ya Dakatar Da Kamfe Har Sai Baba Ta Gani, Ya Bada Dalili

Zaben 2023: Gwamna Sanwo Olu Ya Dakatar Da Kamfe Har Sai Baba Ta Gani, Ya Bada Dalili

  • Biyo bayan kunci da wahala da yan Najeriya suka shiga sakamakon karancin man fetur da sabbin takardun naira, jam'iyyar APC ta Legas ta dakatar da kamfen har sai baba ta gani
  • Gboyega Akosile, babban sakataren watsa labarai na Gwamna Babajide Sanwo Olu na jihar Legas ya sanar da hakan cikin wani rubutu da ya yi a shafinsa na Twitter
  • Hakazalika, shugaban jam'iyyar na APC reshen jihar Legas, Ojelabi, ya ce an dauki matakin ne saboda duba wahalwahalun da yan Najeriya ke ciki

Jihar Legas - Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu na jam'iyyar All Progressives Congress, APC, mai mulki a kasa ya dakatar da kamfen a dukkan ofisoshin sa na siyasa a jihar.

Gboyega Akosile, babban sakataren watsa labarai na gwamnan na Legas ne ya sanar da hakan cikin wani rubutu a Twitter da Legit.ng ta gani a ranar Talata 7 ga watan Fabrairun 2023.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: "Allah Na Dogara Da Shi Domin Nasara," Tinubu Ya Fada Wa Mahalarta Taron Ruwa Da Tsaki Na APC

Sanwo Olu
Zaben 2023: Gwamna Sanwo Olu Ya Dakatar Da Kamfe Har Sai Baba Ta Gani, Ya Bada Dalili. Hoto: @gboyegaakosile
Asali: Twitter

A cewar Akosile, gwamnan da jam'iyyar ta APC sun dauki wannan matakin gaggawan ne saboda kokawa da kan karancin sabbin takardun naira da sabon tsarin babban bankin Najeriya, CBN, na sauya kudi ya haifar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ga abin da ya rubuta a Twitter:

"Gwamna @jidesanwoolu, @OfficialAPCNg, reshen jihar Legas ta dakatar da kamfen har sai baba ta gani saboda halin da ake ciki a kasar na karancin man fetur da takardun kudi.
"Shugaban jam'iyyar APC ya bada hakuri ga mazauna Legas ya kuma yi kira da su kwantar da hankulan su."

Abin da shugaban APC na Legas ya ce game da dakatar da kamfen din

Shugaban jam’iyyar APC na Legas Hon. Cornelius Ojelabi, ya ce an dauki matakin ne "sakamakon yanayin da kasar ke ciki saboda karancin man fetur da radadin da aka yi na sake fasalin Naira."

Kara karanta wannan

Saraki Ya Magantu Kan Zaben Shugaban Kasa Na 2023: Ya Fada Ma Yan Najeriya Abun da Za Su Yi Wa APC

Daily Trust ta rahoto cewa shugaban jam'iyyar APC na Legas din ya jaddada cewa yan jam'iyyar APC ba su da kariya daga wannan ci gaban saboda an yi masa korafi da yawa.

Ya kara da cewa ya hada murya da 'yan Najeriya masu kyakkyawar niyya don yin kira da a sake nazarin manufar sake fasalin Naira don ba ta fuskar dan Adam da kuma rage wahalhalun talakawan Najeriya suka ciki.

Ojelabi ya kuma yi kira da a samar da kayayyakin man fetur domin kada a yi barazana ga shirye-shiryen zaben da kuma rage mummunar tasirin tattalin arziki.

Ya umarci dukkan yan Lagos da su ci gaba da bin doka yayin da za a warware dukkan batutuwan a kan kari.

Shima Ministan Ayyuka da Gidaje, Babatunde Fashola ya ce ba shi da sabbin takardun nairan kuma yan Najeriya na cikin mawuyacin hali.

Tsohon gwamnan na Legas ya bayyana hakan ne cikin wata hira da aka yi da shi a Channels TV.

Asali: Legit.ng

Online view pixel