Tsohon Hafsun Sojoji, Buratai Ya Bayyana ‘Dan Takaran da Yake yi wa Aiki a 2023

Tsohon Hafsun Sojoji, Buratai Ya Bayyana ‘Dan Takaran da Yake yi wa Aiki a 2023

  • Laftana Janar Tukur Yusuf Buratai ya zama cikakken ‘dan siyasa bayan yin ritaya daga gidan soja
  • Hafsun Sojojin Najeriyan tsakanin 2015 da 2020 ya ce Jam’iyyar APC da Bola Tinubu ne zabinsa a 2023
  • Buratai ya ce zai yi kyau a ba Tinubu ya cigaba a kan tubalin da Muhammadu Buhari ya dora tun 2015

Abuja - Tukur Yusuf Buratai wanda ya rike shugaban hafsun sojoji na tsawon lokaci, ya yi kira mutane su marawa jam’iyyar APC da Bola Tinubu baya.

Laftana Janar Tukur Yusuf Buratai mai ritaya ya bayyana wannan lokacin da ya yi wata hira da 'yan jarida a Abuja, Premium Times ta kawo rahoton.

Tsohon shugaban hafsun sojojin ya ce ya shiga siyasa, kuma yana goyon bayan jam’iyyar APC domin a ra’ayinsa tana da nufin taimakawa al’umma.

Kara karanta wannan

Masu Tunanin Akwai Wani Sabani Tsakanina da Buhari Za Su Ji Kunya Inji Tinubu

Rahoton ya ce daga cikin dalilan da tsohon sojan ya bada na shiga APC shi ne ya fi hango nasararta kan sauran jam'iyyun hamayya da ke harin mulki.

“Na kuma yi imani jam’iyyar tana nufin Najeriya da alheri, kuma ta fi samun damar lashe zaben shugaban kasa.
Mu na aiki dare da rana domin tabbatar da cewa Asiwaju Bola Tinubu ya samu nasara a zaben da za a gudanar.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kuma ina mai kira a gare ku da cewa ku zabu wanda ku ke ra’ayi, amma idan ku na son jin ra’ayina, ku zabi APC.

- Laftana Janar Tukur Yusuf Buratai

Jam’iyyar APC
Taron jam’iyyar APC Hoto: @officialasiwajubat
Asali: UGC

INEC za ta iya, a ba APC shekaru 16

People Gazette ta rahoto Laftana Janar Tukur Yusuf Buratai yana kira ga ‘Yan Najeriya da su guji siyasar daba, su bari ayi zabe na adalci da gaskiya.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Tsohon Dan Majalisar Tarayya, Shehu Sani Ya Yi Tsokaci A Kan Masu Juya Aso Rock

Jakadan Najeriyan zuwa kasar Benin yana ganin hukumar INEC za ta shirya zaben kwarai.

Tun da PDP tayi shekaru 16 a kan mulki, Buratai yake cewa akwai bukatar mutanen kasar nan su ba jam’iyyarsu ta APC dama ita ma tayi shekaru 16 a mulki.

Idan APC ba ta tabuka abin komai ba, tsohon hafsun ya ce sai ayi waje da ita. Amma a yanzu yana ganin zai yi kyau a cigaba da bin tafarkin Muhammadu Buhari.

G5 za ta surke a PDP?

A wani rahoto da aka fitar a ranar Talata, an ji labari Gwamnonin da ke yakar Atiku Abubakar sun fara wargajewa ana saura makonni a shiga zaben 2023.

Shugaban PDP na kasa, Dr. Iyorchia Ayu ya ce wani Gwamna da ke cikin ‘Yan G5 ya balled aga tafiyarsu Nyesom Wike, yana goyon bayan Atiku Abubakar.

Kara karanta wannan

Karancin Naira: Babu laifin Buhari, Peter Obi ya ce 'yan Najeriya su hankalta, su yiwa Buhari uzuri

Asali: Legit.ng

Online view pixel