'Yan Bindiga Sun Kashe Malamin Jami’ar Nnamdi Azikiwe da Ke Jihar Anambra

'Yan Bindiga Sun Kashe Malamin Jami’ar Nnamdi Azikiwe da Ke Jihar Anambra

  • An hallaka wani malamin jami’ar Nnamdi Azikiwe a jihar Anambra yayin da yake shirin kai yaransa makaranta da sanyin safiya
  • Shaidun gani da ido sun bayyana yadda lamarin ya faru, da kuma yadda mamacin ya yi kokarin tserewa, amma kwanakinsa sun kare
  • Rundunar ‘yan sanda bata tabbatar da faruwar lamarin ba, amma ta ce za ta yi bincike don gano gaskiyar abin da ya faru

Jihar Anambra - An harbe Anthony Eze, wani lakcara a tsangayar ilimi ta jami’ar Nnamdi Azikiwe da ke Awka a jihar Anambra, Daily Trust ta ruwaito.

An ce Eze yana shirin kai yaransa makaranta ne a lokacin da lamarin ya faru a ranar Talata 7 Faburairu, 2023.

An ce mamacin ya yi kokarin gudu a lokacin, amma ‘yan bindigan suka bi shi suka harbe shi har lahira.

Kara karanta wannan

A ina kika samo: Kowa girgiza, wata mata ta samo damin kudi, tana siyar da N50k a farashin N60k

Yadda 'yan bindiga suka sheke lakcara
'Yan Bindiga Sun Kashe Malamin Jami’ar Nnamdi Azikiwe da Ke Jihar Anambra | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Majiyyoyin sun bayyana cewa, ‘yan bindigan sun zo ne a mota Toyota Corolla, inda suka farmake shi bai ji ba bai gani ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Bayanai daga shaidun gani da ido

A cewar wata majiya:

“Muna nan da safe lokacin da yake tuka motarsa zai fito daga cikin gida sai kawai wata mota Toyota Corolla ta tsaya a daidai kofar gidansa, da ya yi kokarin yin baya, sai suka bi shi suka harbe shi a kirji suka tsere.
“Mun gaggauta kai shi asibitin kwararru na Amaku amma likitan asibitin ya tabbatar da ya mutu.”

Martanin 'yan sanda

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Tochukwu Ikenga ya ce, rundunar bata samu labarin aukuwar wannan lamarin ba, The Nation ta ruwaito.

Sai dai, ya yi alkawarin sanar da manema labarai halin da ake ciki duk sadda rundunar ta binciko kana ta samo bayanai da suka cancanta a ji.

Kara karanta wannan

N100m: An kashe 'yan sa kai a Arewa, Tinubu ya kwashi miliyoyin kudi ya ba iyalansu

Ana yawan samun lokuta mabambanta da ake kashe ma’aikatan gwamnati a Najeriya a gidajensu a jihohi daban-daban na Najeriya.

Tinubu ya tallafawa ahalin wadanda aka kashe a Katsina

A wani labarin kuma, dan takarar shugaban kasa a APC ya gwangwaje ahalin ‘yan sa kai da aka harbe a wani yankin jihar Katsina.

Rahotanni sun bayyana cewa, Tinubu ya kwashi kudi har N100m tare da ba mutanen da aka kashe ahalinsu a jihar.

Ya kuma mika ta’aziyyarsa ga shugaba Buhari da gwamnan jihar bisa wannan mummunan rashi da aka yi a jihar a kwanan nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel