Ayu Ya Bayyana Babban Kusan Tsawagar G5 Da Ya Kai Masa Ziyara Har Gida

Ayu Ya Bayyana Babban Kusan Tsawagar G5 Da Ya Kai Masa Ziyara Har Gida

  • Sanata Iyorchia Ayu, shugaban PDP na ƙasa ya bayyana cewa gwamnan Abiya na gab da barin tafiyar gwamnonin G-5
  • Ayu ya yi ikirarin cewa Okezie Ikpeazu ya kai masa ziyara har gida bayan zaben fidda gwanin dan takarar gwamnan Abiya
  • Shugaban babbar jam'iyyar adawa, wanda yace sun sasanta da Ikpeazu, ya aike da muhimmin sako ga gwamnan Benuwai

Benue - Shugaban PDP na ƙasa, Dakta Iyorchia Ayu, ya ce gwamna Okezie Ikpeazu na jihar Abiya, mamba a tawagar gwamnonin G-5, ya kai masa ziyara har gida.

Ayu yace gwamnan ya ziyarce shi ne bayan ɗan takarar gwamnan da yake goyon baya ya sha ƙasa a zaben fidda gwanin da aka sauya.

Ralin PDP a Benuwai.
Ayu Ya Bayyana Babban Kusan Tsawagar G5 Da Ya Kai Masa Ziyara Har Gida Hoto: Atiku Abubakar
Asali: Facebook

Idan baku manta ba, PDP ta shirya sabon zaben fidda ɗan takarar gwamnan Abiya a zabe mai zuwa bayan mutuwar tsohon ɗan takara, Uche Ikonne, wanda Ikpeazu ya zaba ya gaje shi.

Kara karanta wannan

Sauya Kudi: Da Gaske Gwamnan CBN Na Son Haddasa Rudani a Zaben 2023? Fitaccen Gwamnan Arewa Ya Magantu

Premium Times ta rahoto cewa tsohon shugaban ma'aikatan gidan gwamnatin Ikpeazu, Okey Ahiwe, ne ya samu nasara a sabon zaben da PDP ta shirya.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Mun sasanta da gwamna Ikpeazu - Ayu

Da yake jawabi ga dandazon mahalarta ralin kamfen Atiku a Makurdi, jihar Benuwai ranar Litinin 6 ga watan Fabrairu, 2023, Mista Ayu yace sun sasanta da gwamnan Abiya.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito Ayu na cewa:

"Mun warware sabanin dake tsakanin mu da Ikpeazu kuma zai dawo inuwar mu. Kwana biyu da suka shige ya zo har gidana saboda wanda yake so ya sha kaye a zaben fidda gwani."

Ortom ya rasa madafa inji Ayu

Da yake karin haske kan rigingimin PDP, Dakta Ayu yace gwamna Samuel Ortom na jihar Benuwai, mamba a G-5, ya rasa inuwar da zai fake a halin yanzu.

Kara karanta wannan

Magana Ta Kare, Gwamna Wike Ya Magantu Kan Ɗan Takarar Shugaban Kasa Da Zai Marawa Baya a 2023

Shuagaban PDP na ƙasa ya yi kira ga Ortom ya dawo inuwar uwar jam'iyya domin a haɗa karfi da karfe a sake farfaɗo da ita.

"Ina kira ga ƙanina, gwamna Samuel Ortom ya dawo cikin jam'iyya mu ƙara ginata. Ortom ba shi da wurin zuwa."

Karƙashin jagorancin gwamna Wike na Ribas, gwamnoni 5 da suka kunshi Ikpeazu na Abiya, Seyi Makinde na Oyo, Ortom na Benuwai, Ifeanyi Ugwuanyi na Enugu, su ne mambobin G-5.

Tsagin G-5 sun janye daga goyon bayan ɗan takarar shugaban kasa na PDP, Alhaji Atiku Abubakar, saboda Ayu ya ƙi sauka daga muƙamin shugaban jam'iyya na ƙasa.

A wani labarin kuma Kwana 20 Gabanin Zabe, Atiku Ya Yi Wa Tinubu Babbar Illa da Ka Iya Jawo Masa Rashin Nasara

Wasu manyan kusoshin APC da shugabanni sun tabbatar da sauya sheka zuwa PDP a wurin taron yakin neman zabe a karshen mako.

Da yawa daga cikin masu sauya sheƙar sun bayyana cewa sun gaji da wahalhalu da talauci wanda gwamnatin APC ta ƙaƙabawa mutane.

Kara karanta wannan

Ta Rikice Wa Atiku, Gwamna Wike Ya Tuna Baya, Ya Faɗi Hukuncin da Zasu Yanke Wa PDP a Zaben 2023

Asali: Legit.ng

Online view pixel