Ban Taba Cewa Zan Fito Gaban Kamara Na Fadi Wanda Zan Goyi Baya Ba, Wike

Ban Taba Cewa Zan Fito Gaban Kamara Na Fadi Wanda Zan Goyi Baya Ba, Wike

  • Gwamna Wike ya maida martani ga masu kalubalantarsa game da wanda zai goyi baya a zaben shugaban kasa
  • Wike ya bayyana cewa lokacin da ya yi ikirarin bayyana matsayarsa a watan Janairu, bai ce ga hanyar da zai bi ba
  • Jagoran G5 ya fara takun saka da uwar jam'iyyar PDP ta ƙasa ne kan fafutukar neman daidaito tsakanin kudu da arewa

Rivers - Yayin da ake ta cece-kuce kan gazawarsa na ayyana ɗan takarar shugaban ƙasan da zai marawa baya, Gwamna Nyesom Wike, na jihar Ribas, ya maida martani.

Gwamnan ya ce babu inda aka ji ya sanar da 'yan Najeriya ga hanyar da zai bi wajen ayyana wanda zai marawa baya ya zama shugaban kasa a zaben watan da muke ciki.

Gwamna Wike na Ribas.
Ban Taba Cewa Zan Fito Gaban Kamara Na Fadi Wanda Zan Goyi Baya Ba, Wike Hoto: Nyesom Wike
Asali: Facebook

Channels ta rahoto cewa an zuba wa Wike ido sakamakon tabbatarwan da ya yi cewa a watan Janairu zai bayyana ɗan takarar da ya fi so a zaben shugaban ƙasa.

Kara karanta wannan

Ta Rikice Wa Atiku, Gwamna Wike Ya Tuna Baya, Ya Faɗi Hukuncin da Zasu Yanke Wa PDP a Zaben 2023

Wike na ɗaya ɗaga cikin gwamnonin biyar da ake wa laƙabi da G-5 waɗanda suka tsaya kai da fata suna adawa da tsarin arewa ta kwashe ɗan takarar shugaban kasa da shugaban PDP na ƙasa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Bugu da kari, wannan tawaga da ta kunshi gwamnonin PDP biyar da wasu jiga-jigai, sun tsame hannunsu daga kamfen Atiku bisa hujjar dole a dawo a yi adalci da daidaito.

A ranar Talata tsohon daraktan hukumar NIMASA, Dakuku Peterside, ya kalubalanci Wike ya bayyan ɗan takararsa kamar yadda ya yi alkawari, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Gwamna Wike ya maida masa martani

Gwamnan jihar Ribas ya maida masa martani inda ya ce:

"Har ka isa ka fada mun na bayyana ɗan takarar shugaban kasa da nake so, mataki ɗaya kake da ni? Gazawa da nasara, shin abu ɗaya ne?" Wike ya tambaya a wurin ralin kamfen PDP a Patakwal ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Muna Magana da Su – Atiku Ya Kyankyasa Yiwuwar Haduwa da Kwankwaso ko Obi

"Ku duba mutumin da bai iya tabuka komai a kowace rana, bai san manufar G-5 ba. Ban taba cewa zan kawo Kamara na faɗa muku waye ba. Cewa na yi zan gaya wa mutanen Ribas wanda zasu zaɓa."
"Ban bayyana salon da zan bi wajen bayyana wa ba, ban ce zan kawo shirin kai tsaye na faɗi wanene ba, amma su mutanen Ribas ai sun san wanda nake so."

- Nyesom Wike.

A wani labarin kuma 'Yan Daba da Ake zaton na PDP ne Sun Yi Garkuwa da Dan Takarar Gwamnan APC a Jihar Ribas

Wannan shi ne karo ma biyu da tsagerun 'yan daba suka kai farmaki wurin da aka shirya Ralin kamfe cikin kwana 14 da suka shige.

Ahar yanzu dai ba'a ji ta bakin rundunar yan sanda ba game da sabon harin amma ta yi karin haske kan wani farmakin na daban.

Asali: Legit.ng

Online view pixel