Masu Kada Kuri'a a Ribas Zasu Hukunta Shugabannin PDP, Gwamna Wike

Masu Kada Kuri'a a Ribas Zasu Hukunta Shugabannin PDP, Gwamna Wike

  • Gwamnan Wike ya ce mutanen jihar Ribas zasu hukunta jam'iyyar PDP a zaben 25 ga watan Fabrairu, 2023
  • Nyesom Wike, jagoran gwamnonin G-5 ya ce shugabannin PDP na ƙasa sun nuna basu kaunar Ribas karara a 2022
  • Har yanzun babu zaman lafiya tsakanin Wike da shugabancin PDP na kasa tun bayan zaben fidda gwani

Rivers - Gwamna Nyeson Wike ya ce mutanen jihar Ribas zasu hukunta shugabancin jam'iyyar PDP a babban zaɓen shugaban ƙasa mai zuwa saboda sun yi watsi da su lokacin ambaliya a 2022.

The Nation ta rahoto cewa Wike ya faɗi haka ne ranar Talata a makarantar Firamaren al'umma da ke garin Akinima yayin kaddamar da kamfen PDP a ƙaramar hukumar Ahoada ta yamma.

Gwamna Wike.
Masu Kada Kuri'a a Ribas Zasu Hukunta Shugabannin PDP, Gwamna Wike Hoto: Rivers State Government House
Asali: Facebook

Gwamnan ya yi bayanin cewa ibtila'in ambaliyar ya lalata kauyuka a ƙananan hukumomin Abua/ Odual, Ahoada ta yamma da Ahoada ta gabas, inda ya tafi da gidaje kuma ya kori jama'a daga matsugunansu.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: 'Yan Bindiga Sun Kaiwa Ɗan Takarar Gwamna a 2023 Kazamin Hari, Sun Bude Masa Wuta

Wike ya ƙara da cewa a lokacin jarabawa irin wannan, shugabannin PDP suka kekashe ƙasa suka ki ziyartar yankunan da abun ya shafa su jajanta musu.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A cewar Wike, jagorancin PDP na ƙasa sun ziyarci wasu yankunan da bala'in ya afka mawa a wasu jihohi, wanda za'a fassara hakan da sun tsani Ribas shiyasa suka tsallaketa.

Ya ce duk da haka jihar Ribas ba ta damu ba amma mazaunanta zasu watsa wa PDP ta kasa barkono a ido a babban zabe mai zuwa, kamar yadda Sunnews ta rahoto.

A jawabinsa ya ce:

"Kun shiga jarabawa, babbar jarabawa, Ahoada ta yamna, Ahoada ta gabas da Abua-Odual, jarabawar ambaliyar ruwa, bayan haka suna cewa muna jam'iyya ɗaya, akwai mutun ɗaya daga jam'iyya ta ƙasa da ya kawo ziyara?"
"Amma sun je wasu jihohin, kun ga hakan na nufin basu kaunarmu, idan wani ya ce baya sonka, zaka matsa wa kanka kan abinda ya shafe shi?"

Kara karanta wannan

"Ba Zaman Lafiya" Gwamna Wike Ya Sake Fusata, Ya Maida Zazzafan Martani Kan Abu 1 a PDP

Gwamna Wike ya tabbatar wa mazauna ƙaramar hukumar Ahoada ta yamma cewa gwamnatinsa zata kammala ginin sabunta Sakandiren gwamnati dake Okarki.

Ɗan takarar gwamna ya tsallake rijiya da baya a Ribas

A wani labarin kuma Dan Takarar Gwamna a Jihar Ribas Ya Tsallake Harin Kisan da Yan Bindiga Suka Kai Masa

Wasu miyagun yan daba sun farmaki tawagar ɗan takarar gwamnan SDP a jihar Ribas, Sanata Magnus Abe, ranar Litinin.

Bayanai sun nuka cewa maharan sun lalata wasu motoci amma Sanata Abe ya tsira da rayuwarsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel