APC Ta Dage Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa a Oyo Saboda Karancin Mai Da Naira

APC Ta Dage Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa a Oyo Saboda Karancin Mai Da Naira

  • Jam'iyyar APC ta dage gangamin yakin neman zabenta na shugaban kasa a jihar Oyo har sai baba ta gani
  • Tinubu ya dage kamfen dinsa a Oyo saboda zanga-zangar da ke gudana a jihar sakamakon karancin man fetur da takardun sabbin kudi
  • APC ta ce za ta sanar da sabon rana da zaran an yanke shawara yayin da ta nuna yakinin lashe babban zaben mai zuwa

Oyo - Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta dage gangamin kamfen dinta na shugaban kasa da aka shirya yi a jihar Oyo a ranar Talata, 7 ga watan Fabrairu.

A wata sanarwa da ya saki a ranar Litinin, 6 ga watan Fabrairu, kakakin jam'iyyar a jihar Oyo, Olawale Sadare, ya ce an yanke shawarar jingine kamfen din ne saboda rikicin da ke kewaye da karancin naira da fetur, rahoton The Cable.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Tsaida Kamfe Ana Sauraron Zuwansa, Jam’iyyar APC ta Bada Dalili

Bola Tinubu
APC Ta Dage Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa a Oyo Saboda Karancin Mai Da Naira Hoto: @OfficialABAT
Asali: Twitter

Ana zanga-zanga a jihar Oyo

Ana ta zanga-zanga a yankunan kasar ciki harda jihar Oyo saboda karancin sabbin takardun naira da man fetur.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sai dai kuma, ana tsaka da ci gaban, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci a bashi dan lokaci kadan don daukar babban mataki kan karancin naira.

Da yake magana kan dage gangamin, Sadare ya kara da cewar jam'iyyar za ta ba shugaban kasar lokaci don ya magance damuwar da aka shiga kan lamarin.

Ya ce:

"Muna bukatar ba shugaba Muhammadu Buhari damar yin aiki kan lamarin da kuma tabbatar da ganin cewa zaman lafiya ya dawo, musamman tunda ya shafi rikicin man fetur da takardun kudi.
"A APC reshen Oyo, mun gamsu cewa akwai bukatar yin hakan don kada mu shiga hannun masu adawa da damokradiyya wadanda basa son ayi babban zabe mai zuwa.

Kara karanta wannan

Wa'adin Dena Karbar Tsaffin Naira: Atiku Ya Aika Sako Mai Karfi Ga Gwamnan CBN Emefiele

"Mun yi danasanin sanar da dage gangamin kamfen dinmu na shugaban kasa wanda aka shirya yi a ranar Talata har sai baba-ta-gani.
"An dauki matakin ne duba ga matsalolin da kasar ke fuskanta a yanzu."

Za a sanar da sabon rana nan gaba kadan, APC

Ya kuma ce jam'iyyar za ta sanar da jama'a sabon ranar da za ta yi kamfen din da zaran ta yanke shawara.

Jam'iyyar ta bukaci masu biyayya gareta da su kwantar da hankalinsu sannan ta nuna yakinin samun nasara a babban zaben, rahoton Arise News.

Yan bangar siyasa sun farmaki wajen kamfen din APC a jihar Ribas

A wani labarin, mun kawo cewa wasu da ake zaton yan bangar siyasa ne sun farmaki wajen kamfen din APC a karamar hukumar Omuma ta jihar Ribas.

Asali: Legit.ng

Online view pixel