"Nima Ina Ji A Jiki Na", Minista Mai Karfi A Gwamnatin Buhari Ya Ce Shi Kansa Ba Shi Da Sabbin Takardun Naira

"Nima Ina Ji A Jiki Na", Minista Mai Karfi A Gwamnatin Buhari Ya Ce Shi Kansa Ba Shi Da Sabbin Takardun Naira

  • Tsohon gwamnan Lagos, Babatunde Fashola ya bayyana chanjin kudi a matsayin abin da ya jefa yan Najeriya a kunci
  • Ministan ayyuka da gidajen ya ce shima yana jin abin da ake ji kasancewar shima ba shi da kudi a hannu
  • Shugaba Buhari yace zai dauki matakin da ya da ce akan batun biyo bayan ziyarar da gwamnoni suka kai masa ranar Juma'a

Ministan ayyukan da gidaje, Babatunde Fashola, ya ce yan Najeriya na cikin wani yanayi mai tsanani saboda sabuwar dokar chanjin kudi, yana mai cewa shima ba kudi a hannun sa, Daily Trust ta rahoto.

Tsohon gwamnan na Lagos ya bayyana haka lokacin da ya ke tattaunawa da gidan Talabijin na Channels a shirin Siyasa a yau.

Fashola
"Nima Ina Ji A Jiki Na", Minista Mai Karfi A Gwamnatin Buhari Ya Ce Shi Kansa Ba Shi Da Sabbin Takardun Naira. Hoto: Daily Trust
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Saraki Ya Magantu Kan Zaben Shugaban Kasa Na 2023: Ya Fada Ma Yan Najeriya Abun da Za Su Yi Wa APC

Fashola ya ce sabuwar dokar ba ta amfani a yanzu.

Daily Trust ta ruwaito yadda yan Najeriya ke cigaba da bin dogayen layuka a injinan cirar kudi na ATM ko kuma su dinga biyan kudi mai tsada a hannun masu kasuwancin PoS don samun sababbin takardun kudin.

Bayan gwamnonin jam'iyya mai mulki ta APC karkashin kungiyar gwamnoni (PGF) sun roki Shugaba Buhari da ya bar tsohon kudin da sabon su zagaya hannun mutane locaki daya a Juma'ar da ta gabata, shugaban ya ce zai dauki matakin da ya dace cikin kwana bakwai.

Da ya ke sharhi kan chanjin kudin, Fashola ya ce:

''Abin da zan iya fada dangane da chanjin kudi shi ne ina iya ganin bacin rai. Ina ganin mutane a layin ATM. Ina ganin mutane makare a banki suna kokarin cirar kudaden su.
"Zan iya fadar abin da ake ji. Nima, bani da kudi a hannu na. Bani da shi. Wannan dokar bata aiki a halin yanzu. Tana janyo wahalhalun da ba su kamata ba."

Kara karanta wannan

Karancin Naira: Yadda Masu POS Suka Koma Siyan Kudi Daga Gidajen Mai a Wata Jihar Arewa

Masu hada-hadar POS a Jigawa sun mika godiya ga babban bankin Najeriya, CBN

A wani rahoton kun ji cewa wasu masu sana'ar POS a Jihar Jigawa sun jinjinawa kokarin babban bankin kasa CBN kan rarraba musu takardun sababbin Naira don rabawa al'umma a sassan jihar.

Daily Trust a ranar Lahadi ta ruwaito cewa kowanne mai sana'ar POS ya samu N500,000 na sabuwar Naira inda zasu raba N10,000 ga daidaikun mutane.

Shirin bankin ya zagaye kananan hukumomin jihar 27 da nufin saukakawa mutanen karkara wajen samun sababbin kudin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel