Yan Daba Sun Farmaki Wajen Kamfen Din APC a Ribas, Sun Lalata Kayayyaki

Yan Daba Sun Farmaki Wajen Kamfen Din APC a Ribas, Sun Lalata Kayayyaki

  • Tsagerun yan bindiga sun kai hari wajen gangamin kamfen din jam'iyyar APC a yankin Omuma ta jihar Ribas
  • Ana zaton yan daban siyasa ne suka kai hari wajen taron wanda tun a daren Lahadi, 5 ga watan Fabrairu aka shirya shi
  • Tun a makon jiya ne jam'iyyar ta sanar da cewar akwai wasu da ke barazanar hana ta gudanar da gangamin kamfen din nata

Rivers - Wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kai farmaki wajen kamfen din jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a karamar hukumar Omuma ta jihar Ribas, jaridar Punch ta rahoto.

Yan bindigar da ake zaton yan dabar siyasa ne sun kuma lalata kayayyaki a wajen gangamin yakin neman zaben.

Logon APC
Yan Daba Sun Farmaki Wajen Kamfen Din APC a Ribas, Sun Lalata Kayayyaki Hoto: Thisday
Asali: UGC

Tun daren Lahadi aka shirya wajen taron

Jam'iyyar APC ta shirya wajen gangamin nata a daren ranar Lahadi, 5 ga watan Fabrairu amma yan daban suka kai farmaki sannan suka lalata duk kayayyakin da idonsu ya gani a yau Litinin.

Kara karanta wannan

Yobe Ta Arewa: Kotun Allah Ya Isa Ta Shirya Yanke Hukunci Kan Shari’ar Lawan Da Machina

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa APC ta yi hayar wajen ne bayan umurnin da gwamnatin jihar ta bayar inda ta haramta wa jam'iyyun siyasa amfani da wuraren jama'a ba tare da samun amincewar gwamnati ba, wanda aka ce APC ta ki bi.

Sai dai kuma, jam'iyyar APC reshen karamar hukumar Omuma, ta koka a makon jiya cewa tana samun barazana daga wasu mutane da ba a san ko su waye ba cewa ba za a bar jam'iyyar ta yi kamfen ba a yanki.

Jam'iyyar ta yi kira ga Sufeto Janar na yan sanda da ya kafa kwamiti don samar da tsaro, yana mai cewa ana yi wa yawancin tsarin tsaro a yankin kutse.

Kakakin jam'iyyar, Darlington Nwauju, ya tabbatar da ci gaban yana mai cewa da gaske hakan ya faru.

Buhari ya kadu lokacin da ya ji Ahmad Lawan APC take so ta tsayar, El-Rufai

A wani labari, gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya cika da mamaki lokacin da ya ji cewa Ahmad Lawan, shugaban majalisar dattawa APC ke son tsayarwa a matsayin dan takarar shugaban kasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel