Tinubu Ya Tsaida Kamfe Ana Sauraron Zuwansa, Jam’iyyar APC ta Bada Dalili

Tinubu Ya Tsaida Kamfe Ana Sauraron Zuwansa, Jam’iyyar APC ta Bada Dalili

  • Babu maganar zuwan Asiwaju Bola Ahmed Tinubu zuwa jihar Oyo domin yakin neman zaben 2023
  • Jam’iyyar APC mai adawa a Oyo ta ce karancin man fetur da kudi suka jawo aka dakatar da gangamin
  • Sanarwar kakakin jam’iyyar, Olawale Sadare ya nuna sai a nan gaba ‘dan takaran zai ziyarci Ibadan

Oyo - Jam’iyyar APC mai mulki ta dakatar da yawon yakin neman zaben da za ta gudanar a babban birnin jihar Oyo, Ibadan a makon nan.

Premium Times ta ce an tsara cewa jam’iyyar za ta shirya babban gangamin Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a dakin taro na Mapo da yake Ibadan.

A yau Kakakin jam’iyyar APC na reshen jihar Oyo, Olawale Sadare ya shaida cewa an fasa taron yakin neman zaben Bola Tinubu na ranar Talata.

Kara karanta wannan

Rikicin Cikin Gidan Jam’iyyar APC Yana Kara Fitowa Baro-Baro Daf da Zaben 2023

Mista Olawale Sadare bai sanar da madadin lokacin da za ayi kamfen, amma ya ce jam’iyya ta dauki matakin dakatar da taron sai baba ta gani.

Meya jawo aka fasa kamfe?

An rahoto Mai magana da yawun bakin jam’iyyar a Oyo yana cewa karancin man fetur da rashin kudi ya jawo aka fasa yin gagarumin taron.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Jam’iyyar APC
Bola Tinubu a Nasarawa Hoto: @officialasiwajubat
Asali: Facebook

"Mu na takaicin bada sanarwar jinkirta taron yakin neman zabenmu da a baya aka shirya a gobe (ranar Talata).
An dauki matakin ne la’akari da kalubalen da mutane ke fuskanta kuma a ba shugaban kasa damar shawo kan lamarin.
A jihar Oyo mu na da tabbacin cewa akwai bukatar ayi taron saboda ka da a biyewa wasu da ba su so ayi zabe.
Duk da ba a sa sabon rana ba tukuna, mu na tabbatarwa jama’a Oyo za ta karbi bakuncin Asiwaju Bola Tinubu."

Kara karanta wannan

Miyagu Sun Sace Darektan Yakin Neman Zaben Jam’iyyar APC a Wajen Yawon Kamfe

- Olawale Sadare

Tribune ta rahoto cewa jam’iyyar APC ta reshen Oyo tana mai sa ran ba za a ji kunya ba a lokacin da Bola Tinubu ya zo yawon yakin neman takararsa.

Canjin kudi da gwamnan babban banki ya kawo da kuma rashin man fetur sun jawo abubuwa sun yi cak a kusa duka jihohin Najeriya a halin yanzu.

Cankin kudi ba daidai ba ne - Majalisa

Rahoto ya zo cewa Rt. Hon. Femi Gbajabiamila ya ce saura kiris ya bada umarnin a cafke Mista Godwin Emefiele a dalilin canjin kudi da ya fito da shi.

Femi Gbajabiamila ya nuna Majalisar wakilan tarayya tana neman tursasawa CBN ya janye matakin canjin Nairori kamar yadda Bola Tinubu ya bukata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel