Kwankwaso: Sakamakon Zaben Shugaban Kasa Na 2023 Zai Girgiza Yan Najeriya

Kwankwaso: Sakamakon Zaben Shugaban Kasa Na 2023 Zai Girgiza Yan Najeriya

  • Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NNPP mai kayan marmari ya ce yan Najeriya za su sha mamaki bayan ganin sakamakon zaben 2023
  • Tsohon gwamnan na jihar Kano ya nuna gamsuwa cewa jam'iyyarsa ce za ta lashe zaben yana mai cewa sune suka kusanci talakawan Najeriya kuma suka san matsalolinsu
  • Kwankwason har ila yau ya ce jam'iyyarsa ta NNPP da wasu ke yi wa kallon mara karfi bata da bukatar yin maja da wata jam'iyyar kafin ta samu nasarar lashe zabe

Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar New Nigeria Peoples Party, NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya ce yan Najeriya za su yi mamakin sakamakon zaben shugaban kasa, rahoton The Nation.

Da ya ke nuna kwarin gwiwa cewa shine zai lashe zaben, tsohon gwamnan na jihar Kano ya musanta cewa yana tattauna na hadin kai da dan takarar shugaban jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar gabanin zaben na 25 ga watan Fabrairu.

Kara karanta wannan

Takarar Shugaban Kasa: Ka Janyewa Rabiu Kwankwaso: NNPP Ta yi Kira ga Atiku

Kwankwaso
Kwankwaso: Sakamakon Zaben Shugaban Kasa Na 2023 Zai Girgiza Yan Najeriya. Hoto: The Nation News
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Atiku ya shaida wa BBC Hausa cewa yana tattaunawa da yan takarar NNPP da na Jam'iyyar LP, Peter Obi, yana mai cewa akwai yiwuwar daya cikinsu ya janye ya yi aiki tare da shi.

Amma da ya ke magana a shirin Sunrise Daily a gidan talabijin na Channels, Kwankwaso ya bayyana wannan kalaman a matsayin 'ganganci'.

Jam'iyyar NNPP ce kawai ta san ainihin matsalolin talakawan Najeriya, Kwankwaso

Ya ce jam'iyyar NNPP ce kadai jam'iyya wacce ta san matsalolin talakawan Najeriya domin ta tafi kamfe zuwa karkara ta hanyar amfani da mota don sanin halin da mutane ke ciki.

A cewarsa, abin takaici ne mutanen da ake ganinsu da mutunci za su tafi talabijin su furta karerayi su kunyata kansu domin kawai su tallata yan takararsu.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Kwankwaso Ya Gana Da Atiku Sun Tattauna? NNPP Ta Bayyana Gaskiyar Lamari

Ya ce NNPP na jin dadin yadda wasu jam'iyyun ke mata kallon bata kawo karfi ba, ya kara da cewa ba gaggawa ya ke ba don zama shugaban kasa.

Ya ce jam'iyyar tana da tana da kuri'un da ake bukata domin lashe zabe a karon farko ba sai ta nemi hadin gwiwa da wata jam'iyyar daban ba.

Jagoran Kamfen Din NNPP Sun Fita Daga NNPP

A baya kun ji cewa wasu magoya bayan Rabiu Kwankwaso, dan takarar shugaban kasa na NNPP sun sauya sheka zuwa PDP a Bauchi.

Dr Babayo Liman, jagoran yakin neman zaben NNPP na arewa maso gabas na daga cikin wadanda suka sauya shekan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel