Shugaban Kasa a 2023: Obi Baya Tattaunawa Da Atiku – Kungiyar Yakin Neman Zabensa

Shugaban Kasa a 2023: Obi Baya Tattaunawa Da Atiku – Kungiyar Yakin Neman Zabensa

  • Kungiyar yakin neman zaben jam'iyyar Labour Party ta yi karin haske kan zargin yin hadaka tsakanin Peter Obi da Atiku Abubakar
  • Kungiyar yankin neman zaben Obi-Datti ta karyata ikirarin tattaunawa tsakanin dan takararta na shugaban kasa da takwaransa na PDP
  • Kakakin kungiyar, Yunusa Tanko, ya ce mutane na kokarin coin gajiyar shaharar da Obi ya yi ne kawai

Kungiyar yakin neman zaben Obi-Datti ta mayar da martani ga ikirarin dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar na baya-bayan nan cewa yana tattaunawa da Peter Obi gabannin babban zaben 2023.

A wata hira ta musamman da jaridar Punch, Yunusa Tanko, kakakin kungiyar, ya fito fili ya bayyana cewa Obi baya shirin yin hadaka da takwaransa na jam'iyyar PDP.

Peter Obi da Atiku Abubakar
Shugaban Kasa a 2023: Obi Baya Tattaunawa Da Atiku – Kungiyar Yakin Neman Zabensa Hoto: Mr. Peter Obi/Atiku Abubakar
Asali: Facebook

Mun mayar da hankali wajen kamfen amma babu maganar hadaka da kowani dan takara, LP

Kara karanta wannan

2023: Wasu Masu Son Gaje Buhari Abin Dariya Ne, Gwamnan Arewa Ya Tabo 'Yan Takarar Shugaban Kasa

Tanko ya ce wadanda ke yada wannan hasashe mara tushe balle makama suna kokarin cin gajiyar farin jinin da Obi ke samu ne.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya ce:

"A jiya kafin na bar Numan, babu wani abu mai kama da wannan. Mun mayar da hankali wajen kamfen. Ba mu da masaniya a kan wani abu mai kama da hadaka.
"Ina ganin kawai dai wani na kokarin cin gajiyar tikitin Obi-Datti ne. Yanzu haka muna kamfen a Sokoto kuma za mu kasance a Zamfara."

Muna magana da Obi da Kwankwaso, Inji Atiku

Da farko dai mun ji cewa Atiku ya bayyana cewa a shirye yake ya yi aiki da Obi da takwaransa na jam'iyyar NNPP, Sanata Rabiu Kwankwaso, bayan ganawa da shugabannin biyu domin su marawa kudirinsa baya a zabe mai zuwa.

Atiku ya bayyana haka ne a wata hira da ya yi da sashin Hausa na BBC a ranar Talata, 31 ga watan Janairu.

Kara karanta wannan

Laifin APC Da Ganduje Ne Harin Da Aka Kaiwa Buhari a Kano, PDP Ta Tona Asiri

Dan takarar na PDP ya ce Obi da Kwankwaso ba barazana bane gare shi wajen lashe babban zaben na ranar 25 ga watan Fabrairu.

Kwankwaso zai janyewa Atiku, jigon arewa

A wani labari na daban, wani jigon arewa ya bayyana cewa manyan masu ruwa da tsaki a yankin suna kan tattaunawa da Kwankwaso kan yuwuwar janyewarsa daga takarar shugaban kasa tare da goyon bayan Atiku.

Asali: Legit.ng

Online view pixel