Ba Kama Hannun Yaro: An Fara Bi GidaGida Ana Yiwa Tinubu/Shettima Kamfen a Jihar Nasarawa

Ba Kama Hannun Yaro: An Fara Bi GidaGida Ana Yiwa Tinubu/Shettima Kamfen a Jihar Nasarawa

  • Kungiyoyin goyon bayan APC sun fara bi gida-gida suna tallata Bola Tinubu da Kashim Shettima a jihar Nasarawa
  • A yau Alhamis, 2 ga watan Fabrairu ne aka kaddamar da yakin neman zaben Tinubu/Shettima na gida-gida a yankin Nasarawa ta kudu
  • Tanko Almakura ya nuna karfin gwiwar samawa yan takarar shugaban kasar na APC kaso 60 cikin dari na kuri'un al'ummar Nasarawa

Nasarawa - Wani kwamitin yakin neman zaben Tinubu/Shettima mai zaman kansa wanda ke kunshe da kungiyoyi fiye da 360 ya fara bi gida-gida yana yi wa yan takarar na jam'iyya mai mulki kamfen a jihar Nasarawa.

Jagoran kwamitin a jihar Nasarawa, Mista Yusuf Omaki, ya kaddamar da kamfen din a ranar Alhamis, 2 ga watan Fabrairu a yankin Nasarawa ta kudu a garin Lafia, rahoton PM News.

Kara karanta wannan

Rikicin Cikin Gidan Jam’iyyar APC Yana Kara Fitowa Baro-Baro Daf da Zaben 2023

Shettima da Tinubu
Ba Kama Hannun Yaro: An Fara Bi GidaGida Ana Yiwa Tinubu/Shettima Kamfen a Jihar Nasarawa Hoto: @OfficialABAT
Asali: Twitter

Za mu tabbatar da nasarar APC a zaben 2023, Kungiyoyin goyon baya

Omaki ya ce kungiyoyin za su yi aiki don nasarar dan takarar shugaban kasa na APC, Bola Ahmed Tinubu da dan takarar mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima da sauran yan takara a jihar yayin babban zaben.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa, an fara bi gida-gida ana wayar da kan jama'a daga yankin yammacin jihar, yankin arewacin jihar ya biyo baya, za a kuma rufe da kudancin jihar a yau.

Omaki, wanda shine mataimakin daraktan kungiyoyin na arewa ta tsakiya, ya ce dukkanin kungiyoyin goyon bayan a yankin za su yi aiki ka'in da na'in don tabbatar da nasarar Tinubu da Shettima.

"Kamar yadda kuke gani, wadannan mutanen na nan mambobin kwamitin yakin neman zaben, duk kungiyoyin magoya baya ne; muna da kungiyoyin goyon baya 365 a jihar Nasarawa.

Kara karanta wannan

Kaico: Atiku ya rasa babbar dama, shugaba a jihar su abokin takararsa ya ballo ruwa

"Sun hadu don a wayar masu da kai kan kamfen din gida-gida, za su mayar da sakon ga magoya bayanmu a gida don fara kamfen din."

APC Nasarawa za ta samawa Tinubu da Shettima 60% na kuri'u a jihar, Almakura

A martaninsa, Alhaji Tanko Al-Makura, sanata mai wakiltan Nasarawa ta kudu, ya ce yana da yakinin cewa kungiyoyin za su yi aiki tare dn nasarar Tinubu da Shettima a zabe mai zuwa.

Ya nuna karfin gwiwar cewa APC za ta kawowa Tinubu/Shettima kaso 60 cikin 100 na kuri'un jihar Nasarawa.

Har ila yau, wata kungiyar siyasa mai suna ANIM tare da hadin gwiwar Kaura Pressure Group (KPG), ta fara samawa yan takarar APC goyon bayan jama'a a jihar Kebbi, jaridar The Guardian ta rahoto.

jagoran kungiyar APC ANIM, Alhaji Abubakar Sadiq-Fakai, ne ya bayyana hakan a Birnin Kebbi a wajen tattaunawa tsakanin kungiyar da kungiyoyin magoya bayan APC.

Kara karanta wannan

2023: Da Gaske Atiku Da Peter Obi Za Su Yi Maja? Labour Party Ta Fayyace Gaskiyar Lamari

Ku zabi cancanta ba kabilanci ko addini ba, Kwankwaso ga yan Najeriya

A wani labarin, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NNPP, Rabiu Kwankwaso ya ja hankalin yan Najeriya a kan su zabi cancanta ba tare da la'akari da addini ko kabilanci ba a zaben shugaban kasa na 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel