Ana Karancin Naira, Gwamnati za ta Kara Albashin Shugaban kasa, Gwamnoni da ‘Yan Majalisa

Ana Karancin Naira, Gwamnati za ta Kara Albashin Shugaban kasa, Gwamnoni da ‘Yan Majalisa

  • Hukumar RMAFC ta yi karin bayani a kan makasudin yin gyara a kan albashin ma’aikata da jami’ai
  • Da alama Gwamnatin Najeriya za ta kara albashin masu rike da mukaman siyasa da jami’an gwamnati
  • Shugaban RMAFC ya nuna karin kudin da za ayi zai shafi Alkalai da masu aiki a bangaren shari’a

Ondo - Hukumar RMAFC mai alhakin yanka albashin ma’aikata da jami’an gwamnati, ta kare kanta a kan batun duba albashin jami’ai da masu mukami.

A ranar Larabar nan ne shugaban RMAFC na kasa, Muhammed Shehu ya yi magana a garin Akure da ke jihar Ondo, ya fadi dalilinsu na sake yin nazarin albashi.

Daily Nigerian ta rahoto Muhammed Shehu yana cewa gyara tsarin albashi zai rufe tazarar da ake da ita tsakanin ma’aikatan da ke karbar albashin gwamnati.

Kara karanta wannan

Karancin Naira: Fusatattun Matasa Yan Zanga-Zanga Sun Kai Hari Ofishin Gwamna

Shugaban na RMAFC ya halarci zaman da hukumar ta shirya domin sauraron ta-cewar jama’a a shiyyar Kudu maso yammacin kasar a tsakiyar makon nan.

RMAFC ta zauna da jama'a a Ondo

Tokunbo Ajasin mai wakiltar jihar Ondo a hukumar tarayyar ya wakilci Muhammed Shehu, a nan ne aka ji yana bayanin irin hikimar karin albashin da za ayi.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Rahoton ya ce Cif Ajasin ya tabbatar da hukumarsu za tayi adalci da gaskiya wajen daidaita albashin kamar yadda kundin tsarin mulkin kasa ya yi tanadi.

Shugaban kasa
Shugaban kasa Buhari da Gwamnoni a taro Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

Su wa karin da za ayi zai shafa?

A madadin shugaban hukumar, jami’in ya ce wadanda za su amfana da karin da za ayi sun hada da Shugaban kasa, mataimakin shugaban kasa da Ministoci.

Shehu ya kara da cewa Gwamnonin jihohi, mataimakansu, da kuma Kwamishinoni za su amfana da wannan canjin albashi da gwamnatin tarayya za tayi.

Kara karanta wannan

Rikicin Cikin Gidan Jam’iyyar APC Yana Kara Fitowa Baro-Baro Daf da Zaben 2023

Canjin zai kuma shafi masu bada shawara, ‘yan majalisu da masu rike da mukaman da aka ambata a cikin sashe na 84 da na 124 na kundin tsarin mulkin 1999.

Pulse ta ce hukumar tayi la’akari da halin da tattalin arzikin Najeriya ya shiga a halin yanzu.

Manufar gyaran albashin shi ne a tabbata babu wani ma’aikaci ko jami’i da ake ware shi, ma’ana masu rike da kujerun siyasa da alkalai za su ci moriyar abin.

Bashin N44tr a kan Najeriya

Ku na da labari cewa Hukumar NBS ta fitar da bayanan duka bashin N46tr da ake bin gwamnatin tarayya da jihohi 36, bashin da ake bin Legas ya zarce N800bn.

Kamae yadda alkaluman suka nuna, idan aka tara bashin da ke wuyan Gwamnatocin Kebbi, Katsina da Jigawa ba su kai abin da ake bin jihar Ogun ba

Asali: Legit.ng

Online view pixel