Zaben 2023: Kwankwaso Ya Gana Da Atiku Sun Tattauna? NNPP Ta Bayyana Gaskiyar Lamari

Zaben 2023: Kwankwaso Ya Gana Da Atiku Sun Tattauna? NNPP Ta Bayyana Gaskiyar Lamari

  • Jam'iyyar New Nigeria's Peoples Party, NNPP, ta karyata kalaman Atiku kan batun hadewa da Kwankwaso
  • Mai magana da yawun kwamitin yakin neman zaben Kwankwaso yace Kwankwaso bazai janyewa kowa takara ba
  • Jam'iyyar ta bayyana cewa Kwankwaso ne a kan gaba in aka kula da yadda campaign din Kwankwaso ke gudana

Jam'iyyar NNPP ta ce dan karar shugabancin kasar ta, Rabi'u Kwankwaso, bai hadu ko ya gana da takwaransa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ko wakilansa ba, don yin wata hadaka a babban zabe mai zuwa na 2023.

Mai magana da yawun kwamitin yakin neman zaben Kwankwaso/NNPP, Ladifo Johnson, shine ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba a Abuja.

Atiku da Kwankwaso
Zaben 2023: Kwankwaso Ya Gana Da Atiku Sun Tattauna? NNPP Ta Bayyana Gaskiyar Lamari. Hoto: @MobilePunch
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kara karanta wannan

Zaben 2023: A Shirye Na Ka In Yi Aiki Tare Da Peter Obi Da Kwankwaso, Atiku

Johnson ya ce abu ne a bayyane cewa Kwankwaso yasha gaban sauran yan takarar shugabancin kasa, musamman Atiku.

Ya bayyana cewa Atiku ya fara ''neman madafar dafawa saboda rushewar tafiyar sa!''

Johnson ya ce martanin nasa nada muhimmanci saboda wasu kalaman Atiku ''da suke da alaka da Kwankwaso''.

Ya kuma ce martanin ya zama dole saboda wasu bayanan karya da suke fitowa daga shafukan sada zumunta cewa yan Kwankwasiyya maliyan 3 a yankin Arewa maso Gabas sun koma PDP.

Kakakin ya bayyana hakan a matsayin hanyoyin zamba na yakin neman zaben Atiku don yada labaran karya ga yan Najeriya cewa Kwankwaso zai hade da shi.

Johnson ya ce:

''Gaskiyar lamari ba wata magana tsakanin Atiku da Kwankwaso ko wakilansa kan batun hadewarsu don yin aiki tare.
''Suna haduwa ne kawai in sunje tarukan yada manufa a yan watannin da suka wuce!
''Yan Najeriya zasu iya tuna cewa a sha bayyana labarin karya cewa Kwankwaso na da karfi a iya kano ne!

Kara karanta wannan

2023: Da Gaske Atiku Da Peter Obi Za Su Yi Maja? Labour Party Ta Fayyace Gaskiyar Lamari

''Sai kuma kawai mutum mabiya miliyan 3 suka daina goya masa baya a Arewa masa Gabas?"

Johnson ya sake jaddada cewa Kwankwaso ba zai janye takara ga kowa ba, kuma ba zaiyi aiki da kowanne dan takara ba ko Atiku Abubakar.

Johnson ya cigaba da cewa:

''Muna takarar don yin nasara da kuma daga darajar yan Najeriya.
''Yan adawa da suka gane yadda abin yake daga kasa da kuma yadda yankin neman zaben Kwankwaso ke gudana yanzu sun fahimci, a saura kwana 24 zabe, cewa masu kada kuri'a daga kasa, maza da mata, sun yanke shawarar zabar Kwankwaso da NNPP a matsayin zabi."

Asali: Legit.ng

Online view pixel