Zaben 2023: A Shirye Na Ka In Yi Aiki Tare Da Peter Obi Da Kwankwaso, Atiku

Zaben 2023: A Shirye Na Ka In Yi Aiki Tare Da Peter Obi Da Kwankwaso, Atiku

  • Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana cewa akwai yiwuwar su hade da daya cikin Rabiu Musa Kwankwaso ko Mr Peter Obi
  • Dan takarar na jam'iyyar PDP ya ce babu wanda ke barazana ga nasarar sa amma yana tattaunawa da mutum biyun don cimma matsaya
  • Atiku ya bayyana cewa sun shirya tsaf don tunkurar zabe kuma ko rikicin jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, ba zai hana shi nasara ba

Dan takarar shugabancin kasa a inumar jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa a shirye yake don yin aiki da dan takarar jam'iyyar NNPP, Rabi'u Musa Kwankwaso da kuma na jam'iyyar LP Peter Obi bayan ya tattauna da su game da manufofinsa a babban zabe mai zuwa.

Atiku ya bayyana haka a wata tattaunawar mintuna 15 da yayi da sashen Hausa na BBC ranar Talata.

Kara karanta wannan

2023: Wasu Masu Son Gaje Buhari Abin Dariya Ne, Gwamnan Arewa Ya Tabo 'Yan Takarar Shugaban Kasa

Atiku Abubakar
Zaben 2023: A Shirye Na Ka In Yi Aiki Tare Da Peter Obi Da Kwankwaso, Atiku. Hoto: @MobilePunch
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Da yake magana a tattaunawar, Atiku ya ce daga Obi har Kwankwaso ba wanda zai zamo masa barazana don yin nasara a zaben 25 ga wannan watan.

A cewar Atiku:

''Duk da yake, banga wani abun tsoro a su biyun ba amma muna tattaunawa, kuma tattaunawar zata iya kaiwa ga cimma matsayar da za mu iya hade wa da daya daga cikin su.''

Da yake amsa tambayoyi kan rikicin da ya mamaye PDP, Atiku yace kowacce jam'iyya tana da nata rikicin kamar dai yadda suke dashi suma amma suna ta kokari don kawo karshen rikicin nan ba da jimawa ba.

Atiku ya ce:

''Akwai rikicin cikin gida a kowacce jam'iyya. Muna cigaba da tattaunawa da su. Wasu basa cikin PDP ko wata jam'iyya kuma hakan ba zai sa mu fadi zabe ba saboda a yanzu mun shirya tsaf don shirin zabe.

Kara karanta wannan

2023: A Karshe Atiku Ya Magantu A Kan Fallasar Da Tsohon Hadiminsa Ya Yi Masa Kan Zargin Wawure Kudi

''Zabe yanzu ba kamar a baya bane da gwamna zai fadawa mutane wanda za su zaba, yanzu yanke hukunci a hannun mutane yake."

Asali: Legit.ng

Online view pixel