Shi Kadai Ya San Abin da Ya Hango, Gwamnan APC Ya Fadi Wanene Magajin Buhari

Shi Kadai Ya San Abin da Ya Hango, Gwamnan APC Ya Fadi Wanene Magajin Buhari

  • Rotimi Akeredolu ya halarci taron yakin neman zaben da APC ta shirya a mazabar tsakiyar Ondo
  • Gwamnan na jihar Ondo ya yi ikirarin Bola Tinubu ne zai lashe zaben shugaban kasa da za ayi
  • Akeredolu ya fadawa mutanensa su yi APC sak, ya ce ba su bukatar zaben wani ‘dan takara dabam

Ondo - Gwamna Rotimi Akeredolu ya tabbatarwa mutanen jiharsa cewa ba kowa ba ne zai lashe zabe mai zuwa ba face Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.

Jaridar The Nation a wani rahoto da ta fitar a ranar Litinin, ta ce Mai girma Rotimi Akeredolu ya hango nasarar jam’iyyar APC mai mulki a zaben 2023.

Gwamnan na jihar Ondo ya dage wajen tallata Bola Ahmed Tinubu ga mutanensa, ya yi kira gare su da su zabi wanda zai iya magance matsalolin kasar.

Kara karanta wannan

Wani hanzari: Sirri ya fito, tsohon kakakin majalisa ya ce hadari ne a ba Tinubu ragamar Najeriya

Akeredolu ya yi jawabi a wajen wani gangamin yakin neman zaben ‘dan takaran Sanatan jihar Ondo ta tsakiya da jam’iyyar APC ta shirya garin Ondo.

APC ta yi babban taro a Ondo

Rahoton ya ce mutane da-dama sun halarci taron yakin neman takarar jam’iyyar APC, Shugaban reshen Ondo, Ade Adetimehin ya ji dadin ganin jama’a.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ganin dandazon mutanen da suka yi wa ‘dan takaransu kara, Akeredolu ya ce ya kamata hakan ya jawo su samu kuri’u masu yawa a zabe mai zuwa.

Tinubu
Gangamin Tinubu a Akwa Ibom Hoto: @officialasiwajubat
Asali: Facebook

Akeredolu: APC Sak za ayi a 2023

Baya ga mai neman zama Sanatan, Gwamna Akeredolu ya yi kira ga ‘Yan jihar Ondo da su zabi duka ‘yan takaran da jam’iyyar APC ta tsaida a zaben 2023.

Gwamnan ya kuma mika tutoci ga masu neman kujerun majalisar tarayya da na dokoki. Ku na da labari cewa ba za ayi zaben Gwamna a jihar Ondo ba.

Kara karanta wannan

Bola Tinubu: Yadda Nayi Ta Lallabar Buhari, Har Aka Kara Wa’adin Canza Tsohon Kudi

Akeredolu wanda shi ne Shugaban kwamitin yakin zaben Tinubu-Shettima a jihohin Kudu maso Yamma ya ce APC tayi sa’ar samun irin Bola Tinubu a 2023.

Siyasar naka sai naka!

A rahoton Vanguard, an ji Gwamnan yana ikirarin Tinubu ne kurum ‘dan takaran kujerar shugabancin kasa da zai iya kawo gyara da cigaba a kasar nan.

Tun da har Tinubu daga yankinsu ya samu tikiti, Akeredolu ya ce babu bukatar su tafi neman wani ‘dan takaran da ya fito jihohin Sokoto ko kuwa Adamawa.

A wajen gangamin ne kuma aka sanar da cewa an samu ‘yan siyasa fiye da 350 da suka fice daga jam’iyyar hamayya ta PDP, suka tsallako zuwa APC mai-ci.

Bayanin Aliyu Sabi Abdullahi

Rahoto ya zo cewa Sanatan Arewacin jihar Neja a majalisar dattawa ya ce Muhammadu Buhari yana tare da Bola Tinubu, yana goyon bayansa.

Sanata Aliyu Sabi Abdullahi wanda ya san abubuwan da ke faruwa a jam’iyya mai-ci ya ce babu rashin jituwa tsakanin shugaban kasa da 'dan takaransu.

Kara karanta wannan

Atiku Ya Ankarar da ‘Yan Najeriya, Ya Fallasa ‘Mugun Shirin’ da Tinubu Yake Kullawa

Asali: Legit.ng

Online view pixel