Halin da Ake Ciki Tsakanin Tinubu da Shugaban Kasa – Sanatan APC Ya Fayyace Komai

Halin da Ake Ciki Tsakanin Tinubu da Shugaban Kasa – Sanatan APC Ya Fayyace Komai

  • Aliyu Sabi Abdullahi ya nuna babu rashin jituwa tsakanin Bola Ahmed Tinubu da Shugaban kasa
  • Sanatan ya ce Muhammadu Buhari yana goyon bayan takarar da Bola Tinubu yake yi a zaben 2023
  • Sabi wanda shi ne Mataimakin shugaban masu tsawatarwa a majalisa ya fadi haka a New Bussa

Niger - Mataimakin shugaban masu tsawatarwa a majalisar dattawa, Aliyu Sabi Abdullahi ya yi karin haske kan abubuwan da ke faruwa a jam’iyyar APC.

Daily Trust ta rahoto Sanata Aliyu Sabi Abdullahi yana cewa babu sabanin da aka samu tsakanin Mai girma Shugaban kasa da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.

Wannan bayani akasin abin da mutane suka rika yadawa ne a ‘yan kwanakin nan, bayan wasu kalamai da aka ji sun fito daga bakin ‘dan takaran na APC.

Da ya je kamfe a garin Abeokuta da ke jihar Ogun, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya yi maganganu da yarbaci wanda ake ganin sun nemi su jefa shi a matsala.

Kara karanta wannan

Wani hanzari: Sirri ya fito, tsohon kakakin majalisa ya ce hadari ne a ba Tinubu ragamar Najeriya

Babatun Tinubu a Abeokuta

Bola Tinubu ya fito yana cewa matsalar wahalar man fetur da karancin takardun kudi da aka samu duka yunkurin kawo masa cikas ne a zabe mai zuwa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

‘Dan takaran ya yi karin-haske tuni, ya nuna cewa ba gwamnatin Buhari yake kokarin suka ba.

Taron APC
Taron APC a Uyo Hoto: @officialasiwajubat
Asali: Facebook

Buhari da Tinubu su na tare?

Da Aliyu Sabi Abdullahi mai wakiltar Arewacin Neja a majalisar dattawa ya zanta da ‘yan jarida a New Bussa a garin Borgu, ya yi karin haske kan batun.

Sanata Sabi Abdullahi ya ce Shugaba Muhammadu Buhari yana goyon bayan takarar Bola Tinubu 100 bisa 100, kuma yana ba jam’iyyar APC gudumuwa.

‘Dan siyasar wanda zai bar majalisar dattawa a Mayun 2023 ya ce Buhari yana kokarin ganin Tinubu ya gaje shi ta hanyar nasara a zabe na kwarai.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Jam'iyyar PDP Ta yi Alla-Wadai Da Rajamun Da Aka Yiwa Shugaba Buhari a Kano

Tinubu Magajin Buhari

The Nation ta rahoto Sanatan yana cewa tsohon Gwamnan na jihar Legas shi ne wanda ya fi dacewa ya karbi mulki daga hannun Muhammadu Buhari.

Mataimakin shugaban masu tsawatarwa ya ce ‘dan takaran zai cigaba daga inda gwamnati mai-ci tsaya, ya yi bayani nan ne a filin wasa da ke New Bussa.

Tsawaita wa’adin canza kudi

An ji labarin yadda Bola Tinubu ya bada gudumuwa wajen karin kwanakin da bankin CBN ya yi na canza kudi, Tinubu ya taka rawar gani a bayan-fage.

Da ya ke jawabi a Benin, ‘Dan takaran na APC, ya bayyana mutanen da canjin kudi zai fi shafa, hakan ta sa ya dage wajen lallabar shugaba Muhammadu Buhari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel