Zaben Tinubu a Matsayin Shugaban Kasa Babban Hadari Ne, Dogara Ya Gargadi ’Yan Najeriya

Zaben Tinubu a Matsayin Shugaban Kasa Babban Hadari Ne, Dogara Ya Gargadi ’Yan Najeriya

  • Hon. Yakubu Dogara ya sake jaddada adawarsa ga tikitin Musulmi da Musulmi na jam’iyyar APC mai mulki
  • Tsohon dan majalisar ya shaidawa ‘yan Najeriya cewa, su guji zaban dan takarar shugaban kasa na APC a 2023
  • Dogara dai ya sha nuna adawa da APC tun bayan da Bola Tinubu ya zabi Kashim Shettim a matsayin abokin takara

Jos, Filato – Tsohon kakakin majalisar wakilai ta kasa, Hon. Yakubu Dogara ya gargadi ‘yan Najeriya game da zaban Tinubu a matsayin shugaban kasa.

Gargadinsa na zuwa ne a ci gaba da adawarsa da tikitin Musulmi da Musulmi da APC ta yi a zaben 2023 da ke tafe nan da watanni.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa, Dogara ya yi wannan tsokaci ne a yayin wani taron addinin Kirista da aka gudanar a Jos a ranar Lahadi 30 ga watan Janairu.

Kara karanta wannan

Ahaf: An kuma, Tunubu ya sake yin wata katobarar da tafi na baya game da Atiku

Jigon siyasan na Bauchi ya bukaci ‘yan Najeriya da su nesanci dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmad Tinubu, tare da cewa, ya saba manufar hadin kan Najeriya.

Tinubu ba abin yarda bane, inji Yakubu Dogara
Zaben Tinubu a Matsayin Shugaban Kasa Babban Hadari Ne, Dogara Ya Gargadi ’Yan Najeriya | Hoto: vanguardngr.com
Asali: Facebook

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya kuma bayyana cewa, Tinubu na da bunu a kaba, don haka zai abubuwa marasa dadi ga ‘yan Najeriya idan aka zabe shi.

A cewarsa:

“Wannan ba siyasar kiyayya bace, siyasa ce ta ba da kariya. Siyasa ce ta tsare lafiyar kasa kuma aiki ne na ‘yan kasa.
“A tsarin shugabanci, babu shugaban da zai jagoranci mutane zuwa inda bai taba zuw aba. Wannan mutumin zai samar da abin da shi kansa yake ne, ba wai abin da yake ya yi ba. Duniya ta san waye shi kuma mu ma mun sani.”

Tinubu zai mika Najeriya ga wasu kasashe

Ya kuma bayyana cewa, zaban Tinubu hadari ne, inda yace akwai yiwuwar Tinubu ya ba da ‘yan Najeriya ga kasashen duniya, The Nigerian Lawyer ta tattaro.

Kara karanta wannan

Bola Tinubu: Yadda Nayi Ta Lallabar Buhari, Har Aka Kara Wa’adin Canza Tsohon Kudi

“Zaban shugaban kasan da aka san laifukansa da yawa yana nufin kasashen da ke da shaidar barnarsa ta baya za su bibiye shi. Zai zama kadarar kasashen waje.”

Tinubu dai na yawan yin katobara a maganarsa, kuma hakan na jawo cece-kuce da daukar hankali a idon 'yan Najeriya.

A farkon makon nan Tinubu ya ambaci abokin hamayyarsa da shugaban majalisar dattawa ta Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel