'Barin Zance: Gwamnonin APC 3 Sun Jagoranci Tinubu Domin Kai Wa Buhari Ziyarar Dannar Ƙirji

'Barin Zance: Gwamnonin APC 3 Sun Jagoranci Tinubu Domin Kai Wa Buhari Ziyarar Dannar Ƙirji

  • Asiwaju Ahmed Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar All Progressives Congress, APC, ya ziyarci Shugaba Buhari a Daura, jihar Katsina
  • Hakan na zuwa ne bayan 'babatu' da Tinubun ya yi a wurin kamfen a Abeokuta inda ya ke cewa an kirkiri canjin kudi da karancin man fetur don hana shi cin zaben 2023
  • Jam'iyyar PDP ta yi martanin cewa da Buhari ya ke yi tunda gwamnatin Buhari ne ta yi canjin kudin, amma kwamitin kamfen din Tinubu ta ce Buhari dan takarar na APC ke nufi ba

Katsina - Gwamnoni uku na jam'iyyar APC, a daren ranar Alhamis sun raka Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar, don ganawa da Shugaba Muhammadu Buhari a Daura, Jihar Katsina, rahoton The Cable.

Shugaban kasar ya tafi jihar ne don kai ziyarar aiki na kwana biyu.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Tinubu Ya San Cewa Atiku Ne Zai Zama Shugaban Kasa, In Ji Shu'aibu

Gwamnonin APC da Tinubu
Wasu Gwamnonin APC 3 Sun Raka Tinubu Ziyarar 'Ceton Fuska' Bayan Babatun Da Ya Yi A Abeokuta. Hoto: @thecableng
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ziyarar Tinubu na zuwa ne bayan zafafan maganganu da ya yi yayin ralli dinsa a Abeokuta, babban birnin jihar Ogun, ranar Laraba.

An kirkiri

Dan takarar shugaban kasar na APC ya ce an bulo da sauya takardun naira ne da kirkirar karancin man fetur don kawo masa cikas a takarar shugaban kasa.

Tsohon gwamnan na jihar Legas ya ce:

"A boye man fetur, a boye takardar naira, amma za muyi zabe! za mu yi nasara.
"Ko da kun sauya launin takardun naira, abin da ku ke so ba zai faru ba. Za mu ci zaben. Jam'iyya mai alamar lema za ta sha kaye. Za mu karba wannan gwamnatin daga hannunsu - masu zagon kasa da ke ja da mulki tare da mu."

Kara karanta wannan

Yan Kwanaki Kafin Zabe, Tinubu Ya Daukarwa Iyaye Gagarumin Alkawari Da Zai Cika Masu a Kan 'Ya'yansu

Gwamnatin Buhari Tinubu ke suka, Jam'iyyar PDP

A baya-bayan nan, jam'iyyar PDP ta bayyana kalaman Tinubu a matsayin suka ga gwamnatin Shugaba Buhari.

Amma, kwamitin kamfen din shugaban kasa na APCta ce tsohon gwamnan na Legas bai zargi Buhari ba kan lamarin - kawai ya gargadi masu zagon kasa me da ke yi wa PDP aiki.

Gwamonin APC 3 Da Suka Raka Tinubu Ganin Buhari

Gwamnonin da suka yi wa Tinubu rakiya don kai ziyarar 'ceton fuska' wurin Buhari suna Aminu Masari na Katsina, Abubakar Bagudu na Kebbi, da Babagana Zulum na Borno.

Gwamonin APC da Tinubu
Wasu Gwamnonin APC 3 Sun Raka Tinubu Ziyarar 'Ceton Fuska' Bayan Babatun Da Ya Yi A Abeokuta. Hoto: @thecableng
Asali: Twitter

Dikko Umaru Radda, dan takarar gwamnan na APC a Katsina shima ya tafi ziyarar tare da su.

The Cable ba ta iya sanin abin da ya biyo bayan taron ba.

A watan Yunin 2022, Tinubu ya yi wani babatun - a Abeokuta - inda ya bada labarin yadda ya taimaki Buhari ya samu mulki yana mai cewa yanzu lokacinsa ne.

Kara karanta wannan

Tinubu bai zagi Buhari ba, PDP da wasu yan jarida ke kokarin hada su rigima: Inji APC

Buhari ya gana da Bola Tinubu, Ya Bayyana Dalilin Da Yasa Ba A Gansa Wurin Kamfen Ba

A baya, kun ji cewa Bola Ahmed Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC ya sadu da Buhari a fadar shugaban kasa.

Buhari ya tabbatarwa Bola Tinubu cewa yana tare da shi kuma zai taya shi yakin neman zabe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel