Kamfe Ya Tsaya Babu Shiri Bayan An Kora ‘Yar Takarar M/Gwamna da Ta je Yakin zabe

Kamfe Ya Tsaya Babu Shiri Bayan An Kora ‘Yar Takarar M/Gwamna da Ta je Yakin zabe

  • Funke Akindele ta ziyarci kasuwar kayan marmari da ke Ikosi domin tayi wa jam’iyyar PDP kamfe
  • ‘Yan daba sun aukawa, ‘Yar wasar mai neman zama mataimakiyar gwamnar jihar Legas a zaben 2023
  • Kakakin Jam’iyyar hamayya ta PDP a Legas ya ce ba kowa ya kitsa wannan aiki ba sai Abolanle Bada

Lagos - Funke Akindele mai neman zama mataimakiyar gwamnar jihar Legas a jam’iyyar PDP ta ji babu dadi a wajen wani yawon kamfe da ta je.

Vanguard ta fitar da labari cewa wasu ‘yan banga da dabar siyasa sun kora Funke Akindele a lokacin da ta shiga kasuwar kayan marmari a Ikosi.

A ranar Talata, 25 ga watan Junairu 2023 lamarin ya faru da ‘yar wasan kwaikwayon da ta tsaya neman kujerar mataimakiyar gwamnan 2023 a PDP.

Kara karanta wannan

An Haramtawa Wasu ‘Yan Najeriya Shiga Amurka, Atiku Ya Yi Maza Ya Yi Magana

Da hukumar dillacin labarai na kasa watau NAN ta zanta da ‘dan takaran Gwamnan Legas a inuwar PDP, Abdul-Azeez Adediran ya tabbatar da hakan.

Hakan ya faru - Jandor

Abdul-Azeez Adediran wanda aka fi sani da Jandor ya ce abin da ya faru ya takaita masu yawon kamfe da suka je yi a wannan kasuwa da ke Legas.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Da ya hadu da babban limamin masallacin Ketu, Jandor ya shaida masa an dabawa wani jami’in tsaronsu wuka, sannan aka raunata wasu ‘yan jarida.

Yakin zabe
Taron PDP a 2023 Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

‘Dan takaran ya ce hakan ya sa Akindele ta hakura da yawon kamfe da aka fito, su kuma sauran ‘yan tawagar su ka cigaba da yakin neman zabensu.

Martanin jam’iyyar PDP

Mai magana da yawun bakin jam’iyyar PDP ta reshen jihar Legas, Hakeem Amode ya fadawa Premium Times cewa an tura masu gungun ‘yan daba ne.

Kara karanta wannan

‘Yan bindiga Sun Shiga Gida, Sun yi Nasarar Awon Gaba da Hakimi a Arewacin Najeriya

Hakeem Amode yake cewa sun saba shiga kasuwanni domin tallata jam’iyyar adawa ta PDP ga mata masu kasuwanci, a Ikosi sai aka ci karo da miyagu.

Jam’iyyar PDP ta na zargin shugabar karamar hukumar Ikosi, Abolanle Bada ta kawo ‘yan daba a kasuwar, su ka auka masu saboda su na neman kuri’u.

A Oktoban 2022, Jandor ya koka da an kai masu hari da suka shiga wasu wurare yin kamfe. Amode ya ce sun saba da ganin barazana cikin kasuwanni.

Mubaya'ar Coalition of United Political Parties

An ji labari kungiyar CUPP ta ji dadin yadda Atiku Abubakar yake goyon bayan a canza fasalin kasa, kuma ya yi alkawarin zai karawa jihohi karfi.

Sannan ganin Atiku ya yi mataimakin shugaban kasa kuma ya dauko Kiristan Kudu, Gwamna Ifeanyi Okowa, CUPP ta ce shi za ta marawa baya a 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel