Sa'o'i Bayan Daraktan Kamfen din Tinubu ta bar APC, Ta Ziyarci Atiku Abubakar

Sa'o'i Bayan Daraktan Kamfen din Tinubu ta bar APC, Ta Ziyarci Atiku Abubakar

  • Bayan awanni 72 da tsame hannun da 'yar gwagwarmayar siyasa Naja'atu Muhammad ta jihar Kano tayi daga jam'iyyar APC, ta ziyarci Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP
  • An gano yadda yar gwagwarmayar siyasar ta fitar da takardar murabus daga mukaminta na Daraktar kungiyar kamfen din Tinubu a ranar 19 ga watan Janairu, 2023
  • Naja'atu ta ce jam'iyyun siyasa bata da wani bambanci, suna amfani da rigar siyasa ne don amfanin kansu don haka ita gyara ta ke so ba jam'iyyu ba

Abuja - Fitacciyar 'yar gwagwarmaya kuma 'yar siyasa da ke Kano, Hajiya Naja'atu Muhammad, tayi ribas bayan awanni 72 da fita daga APC gami da bayyana yadda ta daina siyasa.

Siyasar Najeriya
Sa'o'i Bayan Daraktan Kamfen din Tinubu ta bar APC, Ta Ziyarci Atiku Abubakar. Hoto daga leadership.ng
Asali: UGC

Naja'atu, wacce tayi murabus daga mukaminta na Darakta a kwamitin kamfen APC ranar Alhamis, a Abuja, ta hadu da 'dan takarar shugaban kasar jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, a Abuja yammacin Lahadi, inda tayi alkawarin hada kai da tsohon shugaban kasar.

Kara karanta wannan

Makiyan Jihar Bauchi Ne Kadai Za Su Zabi Dan Takararmu, Inji jiga-Jigan APC Da Suka Sauya Sheka Zuwa PDP

Leadership ta ruwaito yadda Naja'atu a wata takarda da ta fita ranar 19 ga watan Janairu, 2023 da tayi ma shugaban jam'iyyar APC na kasa, Abdullahi Adamu, ta ce kalubalen da Najeriya ke fuskanta na bukatarta don fafutukar kawo canji da kasar.

"Na rubuto maka ne don sanar da kai game da murabus din da nayi daga APC.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Haka zalika, a wannan takardar ina mai sanar maka murabus dina daga shugabar Kungiyar kamfen din 'dan takarar jam'iyyar APC. Abun alfahari ne aiki da ku don kawo cigaban gina kasarmu."

- Kamar yadda takardar ta nuna.

Haka zalika, a wata takarda ta daban da ta fita ranar Lahadi, 'yar gwagwarmayar siyasar ta ce jam'iyyun siyasa basa da wani bambanci.

"Bayan tsananin nazari da lura, na yanke shawarar raba gari da jam'iyyun siyasa. Na fahimci cewa, kimata da tunanina ba su yi daidai da jam'iyyun siyasa ba.

Kara karanta wannan

2023: Gwamna Wike Ya Fadi Mummunan Abin Da Zai Faru Bayan PDP Ta Kori Magiya Bayan Gwamnonin G-5

"Jam'iyyun siyasarmu basa da wani bambanci, kawai riguna ne da 'yan siyasa ke sakawa don amfanin kansu da kare ra'ayinsu a wani lokaci.
"Sakamakon haka ne muke ganin 'yan siyasa na canji da wannan rigar zuwa wacce tayi musu daidai."

- A cewarta.

Sai dai, har yanzu babu tabbacin ko Hajiya Naja'atu ta sauya sheka zuwa PDP bane ko kuma kawai tana da ra'ayin marawa Atiku baya a gangamin zabe mai karatowa.

Sai dai, yayin zantawa da Leadership ranar Lahadi, kakakin kungiyar kamfen din Atiku da Okowa, Sanata Dino Malaye, ya tabbatar da yadda Hajiya Naja'atu Muhammad ta kaiwa 'dan takarar shugaban kasar jam'iyyar PDP ziyara ranar Lahadi.

Fitacciyar 'yar siyasar Kano ta bar APC

A wani labari na daban, Sanata Naja'atu Muhammad, daraktan kamfen din Bola AHmed Tinubu a jihar Kano ta bar jam'iyyar APC.

Ta sanar da cewa Najeriya na bukatarta wurin ceto, sake ginawa da farfado da ita don haka jam'iyyun siyasu basu da wannan burin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel