Korar Magoya Bayan Gwamnonin G-5 Daga PDP Ba Zai Haifarwa Jam'iyyar 'Da Mai Ido Ba, Inji Gwamna Wike

Korar Magoya Bayan Gwamnonin G-5 Daga PDP Ba Zai Haifarwa Jam'iyyar 'Da Mai Ido Ba, Inji Gwamna Wike

  • Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas ya fada ma shugaban PDP na kasa, Iyorchia Ayu, cewa yanzu aka saka kafar wando daya tsakanin bangarorin biyu
  • Wike ya yi barazanar cewa tsaginsa zai yi duk mai yiwuwa don bayyana dukkanin zunuban da ake aikatawa a jam'iyyar
  • Har yanzu dai alaka ta ki yin dadi tsakanin shugaban PDP na kasa da gwamnonin jam'iyyar da ke adawa da ci gaba da kasancewarsa a kan wannan matsayi

Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike ya ayyana saka wando daya da shugaban jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) na kasa, Iyochia Ayu kan dakatar da wasu mambobin jam'iyyar.

A cewar gwamnan, dakatar da masu biyayya ga gwamnonin G5 ba zai amfani jam'iyyar PDP da komai ba a babban zaben kasar mai zuwa, jaridar The Nation ta rahoto.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: 'Yan Bindiga Sun Bude Wa Motar Ɗan Takarar Gwamna Wuta

Ayu da Wike
Rikicin PDP: Dakatar da Mutane Ba Zai Taimake Ka Ba, Wike Ga Ayu Hoto: Leadership
Asali: Facebook

Yanzu aka fara rikcin, Wike ga Ayu kan dakatar da jiga-ginan PDP

Gwamnan ya ce da wannan mataki da shugaban jam'iyyar na kasa ya dauka na baya-bayan nan, yanzu aka fara rigima tsakaninsu da Ayu inda ya yi alkawarin kalubalantar matakin da ya dauka a kotu.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cewar Wike, wannan hukuncin baya-bayan nan da Ayu ya dauka duk shirme ne, yana mai cewa sun fi karfin irin wannan matakin.

Gwamnan ya ce:

"Dakatar da mutane da kake yi ba zai taimake ka ta ko'ina ba. Mun sa kafar wando daya da kyau a yanzu. Yanzu haka da nake magana da ku za mu yi duk abun da ya dace bisa doka don kalubalantar duk matakin da muka san cewa baya bisa doka."

Wike ya ce shirme ne shugaban PDP na kasa ya yarda cewa zai iya yiwa mutane barazana ta hanyar dakatar da su, rahoton Within Nigeria.

Kara karanta wannan

Shugaban Jam'iyyar PDP Ya Kwanta Dama Yayin Da Ake Tsaka Da Yakin Neman Zabe

Gwamnan na Ribas, wanda shine shugaban gwamnonin G5 ya ce tsaginsa ya fi karfin irin wannan barazana, yana mai cewa sun yarda da doka da kuma kundin tsarin mulkin jam'iyyar.

A cewar Wike, Ayu na daukar hanyar da za su kara masa ciwon kai a gaba kuma suna kallonsa don sanin mataki na gaba da za su dauka.

Ya kara da cewa:

"Kana aikata abun da zai kara maka ciwon kai a iya sanina da zaben nan. Muna kallonka kuma muna jira ka sanar da karin abokaina. Idan mutum ya ce ba za ka yi bacci ba, shin shima zai yi bacci? Shin Ayu zai yi bacci?"

Sanatan PDP da aka dakatar ya magantu

A halin da ake ciki, jigon PDP da shugabancin jam'iyyar ya dakatar, Chimaroke Nnamani, ya ce lamarin ya matukar daure masa kai.

Ana dai zargin Nnamani wanda tsohon gwamnan jihar Enugu ne kuma sanata mai ci da yiwa babbar jam'iyyar adawar kasar zagon kasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel