Gogaggar 'Yar Siyasar Kano, Naja'atu Muhammad ta Bar Jam'iyyar APC

Gogaggar 'Yar Siyasar Kano, Naja'atu Muhammad ta Bar Jam'iyyar APC

  • Fitacciyar 'yar siyasa a jihar Kano, Sanata Naja'atu Muhammad, ta tattara komatsanta ta bar jam'iyyar APC
  • Tsohuwar Sanatan ta sanar da cewa, dukkan jam'iyyun siyasa a fadin kasar nan daya suke don basu da banbanci ko kadan
  • Tace tana da burin ganin an samu daidaito da cigaba a fadin kasar nan saboda cike ta ke da kalubale, don haka ba zata tsaya a jam'iyya ba

Kano - Naja'atu Muhammad, tsohuwar sanata da ta taba wakiltar Kano ta tsakiya, ta bar jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Daily Trust ta rahoto.

A wata takarda da ta fitar ranar Asabar, Muhammad tace jam'iyyyu a fadin kasar nan basu da wani banbancin akida inda ta kara da cewa jam'iyyu mabanbanta kamar tufafi ne da 'yan siyasa suka saka don wata bukata ta kansu kebantacciya.

Kara karanta wannan

Kwankwaso Ya Tono Asalin Matsala, Ya Fadi Abu Ɗaya Tak Da Ya Kawo Yan Bindiga Arewacin Najeirya

'Yar siyasan tace ta mayar da hankali wurin goyon bayan jama'a da ke da burin shawo kan matsalar kasar nan tun daga tushe a Najeriya, jaridar The Cable ta rahoto.

Naja'atu Muhammad
Gogaggar 'Yar Siyasar Kano, Naja'atu Muhammad ta Bar Jam'iyyar APC. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC
"Fita daga siyasar jam'iyyu a wannan lokacin ya na daya daga cikin wadannan matakan. Dukkanmu mun gane cewa Najeriya ta na fuskantar kalubale daban-daban da suka hada da rashin tsaro, talauci, rashin daidaito da rashin samun abubuwan bukata."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

- Tace.

"Wadannan kalubalen suna bukatar gamsassaun kokari na gogaggau kuma shugabanni masu kishin kasa a dukkan matakan gwamnati.
"Dole ne 'yan Najeriya sun san cewa akwai yuwuwar shiga matsanancin hali bayan sun kori shugabanni da suka gaza a kasar nan a cikin shekarun da suka wuce.
"Dole ne 'yan Najeriya sun san abinda hukuncinsu da zabinsu zai iya haifarawa. Don haka, ajiye zabin ka a jam'iyya daya na iya zama hatsari ga cigaban kasar mu da damokaradiyyarmu.

Kara karanta wannan

Kwankwaso: Manyan Kura-Kurai Aka Tafka, Rashin Shugabanci Na Kwarai a Kasar Nan na Shekaru 24 ne ya Tsundumata Halin da Muke Ciki

"A matsayin 'yar Najeriya da ke yakin neman tabbatar da Najeriya tagari, na mayar da hankali wurin gwagwarmayar samun al'umma mai cike da adalci da daidaito. Na yarda cewa dukkan 'yan Najeriya sun cancanci damar yin rayuwa mai cike da girma, tsaro da dama."

- Naja'atu tace.

'Dan takarar gwamnan LP a Jigawa ya koma APC

A wani labari na daban, ana sauran kwanaki kadan zaben 2023, Yusuf Tsoho, 'dan takarar gwamnan jihar Jigawa a karkashin jam'iyyar LP, ya tattara ya koma jam'iyyar APC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel