Mutanen Mahaifar Dan Takarar Gwamna a APC Sun Fatali da Shi, Sun Rungumi PDP

Mutanen Mahaifar Dan Takarar Gwamna a APC Sun Fatali da Shi, Sun Rungumi PDP

  • An samu gagarumin baraka a tsakanin mambobin jam'iyyar APC a jihar Bauchi ana gab da shiga watan Zabe
  • Mutanen mahaifar Ambasada Saddique Baba Abubakar, dan takarar gwamnan APC a Bauchi sun yi watsi da shi
  • Mambobin jam'iyyar a garin Abubakar sun sauya sheka inda suka hade da jam'iyyar PDP

Bauchi - Kasa da makonni shida kafin babban zaben 2023, jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta rasa mambobinta a jihar Bauchi inda suka koma jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

Nigerian Tribune ta rahoto cewa wasu dubban magoya baya da mambobin APC sun yi watsi da dan takarar gwamnan jam'iyyar a jihar, Ambasa Saddique Baba Abubakar.

Bala Mohammed da Saddique Abubakar
Mutanen Mahaifar Dan Takarar Gwamna a APC Sun Fatali da Shi, Sun Rungumi PDP Hoto: Bala Mohammed
Asali: Facebook

Legit.ng ta tattaro cewa mambobin APC da magoya bayanta a yankin karamar hukumar Giade inda daga nan ne Abubakar ya fito, sun ayyana cewa sun bar jam'iyyar ne saboda basu gamsu cewa dan takarar na da wani abun kirki da zai gabatar ba.

Kara karanta wannan

2023: Gwamna Wike Ya Fadi Mummunan Abin Da Zai Faru Bayan PDP Ta Kori Magiya Bayan Gwamnonin G-5

An nakalto kakakin masu sauya shekar, Umar Mohammed, yana cewa koda dai Abubakar na ikirarin cewa daga yankin ya fito, babu wani abun nuna wa da ke tabbatar da kasancewarsa dan wannan yanki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ayyana cewa yawancin mutanen da suka fito daga karamar hukumar sun yanke shawarar hadewa da PDP don tabbatar da ganin cewa jam'iyyar ta yi nasara a zaben sannan ta ci gaba da kyawawan ayyukanta.

Da yake martani ga sauyin shekar, Darakta Janar na kwamitin yakin neman zaben PDP, Farouk Mustapha ya bukaci masu sauya shekar da kada su zabi dan takarar na APC, yana mai ikirarin cewa babu wani abu da zai yi.

Makiyan jihar Bauchi ne kada za su zabi APC

Leadership ta kuma rahoto cewa Mustapha ya ayyana cewa makiyan jihar ne kadai za su kada kuri'unsu ga dan takarar gwamnan APC.

Kara karanta wannan

Ba'a Ga Keyar Dan Takarar Jam'iyyar ADP Na Gwamna A JIhar Kaduna A Wajen Muhawara Da BBC Hausa Ta Shirya

Ya ce:

"Mu na nan tare da dan takararmu na gwamna, Sanata Bala Mohammed Abdulkadir, da sauran yan takarar jam'iyyarmu, rukunin kamfen dinmu ya kama daga dan takararmu na shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar har zuwa yan takarar kujerar yan majalisa."

Mustapha wanda ya nuna godiya ga mutanen Giade kan zabar PDP a 2019, ya yi gargadi masu zabe a kan zabar APC da sauran jam'iyyun siyasa.

Yanzu za mu fara, Wike ya aike da gagarumin gargadi ga Ayu

A wani labarin, gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike ya ce a yanzu ne za su saka kafar wando daya da shugaban PDP na kasa, Iyorchia Ayu kan dakatar da wasu na hannun damarsa.

Wike ya ce dakatar da masu biyayya ga gwamnonin G5 da Ayu ya yi ba zai amfani PDP da komai ba a zabe mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel