Gwamnatin Ganduje Ta Jawo Farfesa Jega, Ta Hada Shi da Wani Babban Nauyi a Najeriya

Gwamnatin Ganduje Ta Jawo Farfesa Jega, Ta Hada Shi da Wani Babban Nauyi a Najeriya

  • Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya kaddamar da kwamitin da zai duba rikicin makiyaya da manoma
  • Gwamnan jihar Kano ya nada Farfesa Attahiru Jega a matsayin wanda zai jagoranci aikin kwamitin
  • Tsohon shugaban na jami’ar Bayero da ke Kano da wasu mutum 27 za su kawo mafita a kan lamarin

Kano - Mai girma gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje yana ganin adawar siyasa ta taimaka wajen gaza magance rigimar makiyaya da monoma.

A ranar Juma’a, The Nation ta rahoto Abdullahi Umar Ganduje yana bayanin abin da ya jawo sabanin da ke tsakanin manoma da makiyaya ya ci tura har yau.

Gwamnan na jihar Kano ya daura laifin a kan rashin kokarin shugabannin siyasa, karancin kudi, rashin tsaro da karancin sanin aiki a matsayin dalilan.

Kara karanta wannan

Kamfen zub da jini: An sheke wani, da dama sun jikkata a kamfen PDP a wata jihar APC

A cewar Abdullahi Umar Ganduje, gurguwar fahimta da annobar COVID-19 da kuma yarjejeniyar ECOWAS sun taimaka wajen rikicin da ake ta fama da shi.

Yadda aka kawo gwamnati cikas - Ganduje.

Ganduje yana ganin gwamnati tayi hobbasa a kan lamarin a shekarar 2019, amma abin ya faskara. Gwamnan yana ganin tsarin RUGA abu ne mai kyau.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A jawabinsa, Gwamnan ya nuna tsarin da gwamnatin tarayya ta fito da shi a wancan lokaci zai magance matsalar, amma wasu suka yi mummunar fassara.

Attahiru Jega
Farfesa Attahiru Jega Hoto: 21stcenturychronicle.com
Asali: UGC

Ganduje ya ce bai goyon bayan a bar makiyaya su na yawo da dabbobi, sai dai a yarjejeniyar ECOWAS, babu dalilin haramta bala-guro a yammacin Afrika.

Gwamnan ya yi wannan bayani a wajen nada wani kwamiti da zai duba matsalar kiwo da nufin kawo gyare-gyaren da za a bi domin a iya samun zaman lafiya.

Kara karanta wannan

2023: Gwamnn Arewa Ya Tona Asirin Tsagin Dake Hana Ruwa Gudu a Kokarin Sulhunta PDP da Gwamnonin G-5

Kwamitin Farfesa Attahiru Jega

The Cable ta ce tsohon shugaban hukumar zabe na kasa watau INEC, Farfesa Attahiru Jega zai jagoranci aikin da wannan kwamiti mai mutum 27 zai gudanar.

Kwamitin Farfesa Jega yana kunshe da mutane irinsu Dahiru Amin, Muhammad Yahaya Kuta, Martins-Oloja, Bashir Haruna Usman, da M. D. Abubakar.

Sauran ‘yan kwamitin su ne Kabiru Ibrahim, Rabe Mani, Aminu Daneji, Isma’ila Zango, Bello Kaoje, Winnie Solarin, Musa Nuhu da kuma Isa Yuguda.

Fetur ya tashi a gidajen mai

A wata sanarwa da gwamnatin tarayya ta aikawa ‘yan kasuwa, an samu labari a karshen makon nan cewa an umarce su da suka kara kudin fetur.

An fahimci cewa a maimakon N170, za a rika bada sarin litar man fetur a tashoshi a kan N185. Dole abin da ake saida fetur a gidajen mai ya tashi kenan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel