Zan Kawo Maku Sabuwar Rayuwa, Tinubu Ya Nemi Kuri'un Yan Jigawa

Zan Kawo Maku Sabuwar Rayuwa, Tinubu Ya Nemi Kuri'un Yan Jigawa

  • Ɗan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Bola Tinubu, ya ja hankalin mazauna Jigawa su zabe shi
  • A wurin ralin APC, Tsohon gwamnan Legas din yace idan ya zama magajin Buhari zai sauya rayuwar al'umma ta yi kyau
  • Manyan jiga-jigan APC da suka ƙunshi gwamnoni sun halarci gangamin wanda ya gudana ranar Asabar 21 ga watan Janairu

Jigawa - Ɗan takarar shugaban kasa a inuwar All Progressive Congress (APC), Bola Ahmed Tinubu, ya ja tawagar yakin neman zabensa zuwa jihar Jigawa ranar Asabar, kamar yadda Channels ta ruwaito.

A wurin ralin kamfen da aka shirya masa a Jigawa, Tinubu ya yi alƙawarin sama wa mutane kyakkyawar rayuwa idan har aka zaɓe shi ya zama shugaban kasa a watan Fabrairu.

Taron APC a Jigawa.
Zan Kawo Maku Sabuwar Rayuwa, Tinubu Ya Nemi Kuri'un Yan Jigawa Hoto: Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook
"Idan kuka zabe ni ku sani kun zabi ci gaba, kun zabi haɓaka, kun zabi inganta kasuwancin noma, kun zaɓi samun wutar lantarki mai ɗorewa, kun zabi kyakkyawar rayuwa da ilimi mai kyau."

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Jerin Manyan Jihohi 2 da APC Ke Shirin Kwacewa Daga Hannun PDP da Dalili

"Zaku samu kiwon lafiya mai kyau kuma zaku samu kwanciyar hankali," inji Tinubu a wurin gangamin jihar arewa maso yamma ranar Asabar 21 ga watan Janairu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Tsohon gwamnan jihar Legas din ya halarci Ralin tare da rakiyar manyan makusantansa a arewacin Najeriya ciki har da gwamnoni.

Gwamnonin da suka je wurin sun hada da, Babagana Zulum na Borno, Mai Mala Buni na Yobe, Abdullahi Ganduje na Kano, Bello Matawalle na Zamfara, Simon Lalong na Filato da Atiku Bagudu na Kebbi.

A nasa jawabin mai masaukin baki kuma gwamnan jihar Jigawa, Muhammad Badaru, ya roki mazauna jihar su jefa wa Tinubu kuri'unsu domin ci gaba da ayyukan ci gaba.

Badaru ya bayyana cewa har yanzun 'yan Najeriya sun yi amanna da jam'iyyar APC, don haka akwai bukatar mutane su kaɗa mata kuri'unsu.

Kara karanta wannan

Kwankwaso: Manyan Kura-Kurai Aka Tafka, Rashin Shugabanci Na Kwarai a Kasar Nan na Shekaru 24 ne ya Tsundumata Halin da Muke Ciki

Ya ce APC ta aiwatar da tsare-tsare da shiri kala daban-daban da suka taɓa rayuwar 'yan Najeriya musamman masu ƙaramin karfi, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

Wasu Kusoshin APC Sun Yi Sama da Faɗi da Kudin Shirya Ralin Tinubu a Taraba

A wani labarin kuma Wasu Jiga-Jigan APC Sun Cinye Kudin Ralin Bola Tinubu a Jihar Taraba

Kodinetam kamfe ya zargi wasu masu faɗa aji a siyasar jihar Taraba da yin sama da faɗi da kudaden Ralin Bola Tinubu/Shettima.

A ranar 20 ga watan Janairu aka shirya gudanar da Rali a jihar amma jam'iyyar APC ta sanar da ɗage gangamin jihar sai nan gaba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel