Asiri Zai Tonu, ‘Yan Sanda Sun Cafke Jigon APC Shi Kadai Dauke da Katin PVC Rututu

Asiri Zai Tonu, ‘Yan Sanda Sun Cafke Jigon APC Shi Kadai Dauke da Katin PVC Rututu

‘Yan sanda sun yi ram da wani ‘dan shekara 45 yana dauke da katin PVC a garin Dawakin Tofa a jihar Kano

Ana zargin Tasiu Abdullahi Hayin Hago ya shaida cewa Abba Ganduje ya sa ya tattaro masa katin zaben mutane

SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce sun mika wanda aka kama zuwa babban ofishin CID domin a karasa bincike

Kano - Jami’an ‘yan sandan reshen jihar Kano sun cafke wani mai shekara 45 da ake zargi da sayen katin zabe a garin Dawakin Tofa da ke Kano.

Solacebase ta ce an cafke wannan mutumi mai suna Tasiu Abdullahi Hayin Hago ne a unguwar Hayin Doka a karamar hukumar ta Dawakin Tofa.

Ana zargin Tasiu Abdullahi Hayin Hago da sayen katin PVC da boye su, yana jiran lokacin zabe. Jam’iyyar APC ta nuna ba ta da masaniyar batun.

Kara karanta wannan

Abba Kyari Ya Yi Mani Alkawarin N10m Domin Yi Wa Bukola Saraki Sharri – ‘Dan Fashi

‘Yan sanda sun bada sanarwar cewa sun cafke wannan mutumi ne bayan an same shi dauke da katin zabe na PVC 29 da ake zargin na jama’a ne.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sunan Abba Ganduje ya fito

A wani rahoton, an nuna cewa Abba Ganduje ya sa mutumin mai shekara 45 tattaro masa kuri’un wasu daga cikin mazauna karamar hukumar.

Abba Ganduje shi ne mai takarar kujerar ‘dan majalisar wakilan tarayya mai wakiltar Dawakin Tofa, Rimingado da Tofa a karkashin APC mai mulki.

APC a Kano
Taron kamfe na APC a Kano Hoto: @aaibrhim1
Asali: Facebook

Idan ta tabbata gaskiya ne, wanda aka cafke ya shaida cewa Abba Ganduje ne yake bukatar katin wadannan mutane domin ya tallafa masu da N100, 000.

Wanda ake zargin ya bukaci a maido masa katin da ya tattara domin ya cigaba da aikin da yake yi na nemowa ‘dan takaran APC wadanda za su zabe shi.

Kara karanta wannan

Doka a hannu: Kiristoci a jihar Arewa sun fusata, sun kone ofishin 'yan sanda saboda abu 1

...Magana ta je gaban CID

A wata hira da aka yi da shi, kakakin rundunar ‘yan sandan Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar da cewa an mika Hayin Doga zuwa CID.

SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce za ayi bincike a babban ofishin ‘yan sanda na CID a Kano.

Za mu shiga kotu - NNPP

A wani jawabi da ya fitar, kakakin jam’iyyar NNPP na reshen Kano, Sunusi Dawakintofa ya ce za su kai maganar gaba domin gurfanar da mutumin.

Daily Nigerian ta ce Dawakintofa ya ce a baya sun yi nasara a kan wani shugaban APC a Yautar Arewa a yankin Gabasawa da aka samu da irin wannan laifi.

Daniel Obo ta karbi Daniel Obo

A daidai mintin karshe, sai aka ji labari ‘dan takaran SDP na kujerar mataimakin Gwamna a zaben 2023, ya shiga Jam’iyyar APC a jihar Kuros Riba.

Makonni suka rage a shiga filin zabe, ‘dan takara ya bi Bola Tinubu zuwa APC, Daniel Obo ya ce ganin yadda ake tafiya da matasa ne ya kawo ra’ayinsa.

Kara karanta wannan

Sharri aka min: Dan sandan da bindige lauya mai juna biyu ya musanta zargin kisa

Asali: Legit.ng

Online view pixel