2023: Yadda Mutane Suka Kusa Jawo Atiku Abubakar Ya Fashe da Kuka a Wajen Kamfe

2023: Yadda Mutane Suka Kusa Jawo Atiku Abubakar Ya Fashe da Kuka a Wajen Kamfe

  • ‘Dan takaran PDP, Atiku Abubakar da mutanensa sun dura jihar Ekiti domin kamfe a ranar Talata
  • Mafi yawan ‘Yan takaran PDP da Shugabannin Jam’iyyar PDP na Ekiti sun ki zuwa wajen taron
  • Amma kuma duk da haka talakawa da sauran mutanen gari sun yi dandanzo domin ganin Atiku

Ekiti - Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose bai cikin mutanen da suka halarci taron yakin zaben da jam’iyyar PDP ta shirya a ranar Talata.

Ayodele Fayose da mutane tara da ke takarar kujerar majalisar wakilan tarayya sun ki halartar taron yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyarsu.

The Nation ta ce ‘yan takara 26 da ke harin majalisar dokokin da wasu daga cikin shugabannin PDP na reshen Ekiti ba su je wajen taron kamfen din ba.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Yaƙin Da APC Da PDP Ke Yi Ya Ɗauki Sabon Salo Yayin Da Tinubu Ya Tona Babban Ajandar Atiku

Atiku Abubakar ya yi taron yakin neman zabe ne a filin Ekiti Parapo Pavillion a garin Ado-Ekiti.

Rikicin G5 da Atiku ya yi tasiri

Punch tace wadanda suka kunyata Atiku Abubakar su na tare da tsohon Gwamna Ayo Fayose a rikicin da ake yi tsakanin Atiku Abubakar da ‘Yan G5.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Duk da rashin manyan ‘yan siyasa a wajen taron, dinbin mutane da ke goyon bayan jam’iyyar adawar da kuma Alhaji Atiku Abubakar sun halarci taron.

Atiku Abubakar
Atiku Abubakar a Ekiti Hoto: @Atiku.org
Asali: Facebook

Kafin zuwan ‘dan takaran shugaban kasa, ana zargin sai da aka hana abubuwan hawa yawa a jihar.

Atiku ya ji dadin ganin jama'a

The Cable ta ce da yake jawabi, Atiku Abubakar ya yabi mutanen Ekiti da suka yi dandazo domin su hadu da shi duk da yakarsa da gwamnatin APC take yi.

Bugu da kari, ‘dan takaran shugaban kasa ya zargi gwamnati da kirkiro wahalar man fetur da gan-gan saboda a kawo cikas wajen ziyarar kamfe da zai zo.

Kara karanta wannan

Atiku Ya Tona Asirin Manyan Yan Takara Biyu, Yace Hatsari Ne Babba a Zabe Su a 2023

Saura kiris Wazirin Adamawa ya fashe da kuka saboda yadda ya ga taron jama’a, ya ce wannan ya nuna baya ga ilmi, mutanen Ekiti su na da ra’ayin kansu.

‘Dan takaran ya ce ya ji dadin yadda ya samu kyakkyawar tarba, ya yi alkawarin zai gyara hanyoyin zuwa Ekiti idan har ya zama shugaban Najeriya.

Badakalar CBN

An ji labari cewa ‘Dan Majalisar nan, Muhammad Gudaji Kazaure ya fito fili ya fadawa Duniya irin ‘barnar’ da ake tafkawa a boye a babban banki.

Hon. Muhammad Gudaji Kazaure ya bayyana yadda Gwamnan babban banki, Godwin Emefiele ya saye manya, ya ce a boye ake kawo kasafin CBN.

Asali: Legit.ng

Online view pixel