Akwai Hatsari Mai Girma Tinubu Ko Peter Obi Su Karbi Najeriya, Atiku

Akwai Hatsari Mai Girma Tinubu Ko Peter Obi Su Karbi Najeriya, Atiku

  • Mai neman zama shugaban kasa a inuwar PDP ya gargadi yan Najeriya kan hatsarin mika gobensu ga Tinubu ko Obi
  • Alhaji Atiku Abubakar ya ce ya kamata yan Najeriya su kula da mutanen dake babatu a kakar zabe ba komai ne gaskiya ba
  • Masu sharhi kan siyasan sun kayyade yan takarar shugaban kasa zuwa 3, Atiku, Tinubu da Peter Obi

Lagos - Dan takarar shugaban kasa a inuwar jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, yace hadari ne mai girma 'yan Najeriya su miƙa gobensu hannun manyan abokan hamayyarsa a zaben 2023.

Masu sharhi kan harkokin siyasa sun ce gwabzawa zata yi dumi ne tsakanin Atiku, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu na APC mai mulki da Peter Obi na Labour Party.

Atiku Abubakar.
Akwai Hatsari Mai Girma Tinubu Ko Peter Obi Su Karbi Najeriya, Atiku Hoto: Atiku
Asali: UGC

Da yake jawabi a wurin taro kan tattalin arziki da Nigeria Economic Summit Group (NESG) ta shirya a Legas ranar Litinin, Atiku yace ya gama karanta da fahimtar kalubalen da suka addabi Najeriya.

Kara karanta wannan

Bidiyoyi: Emilokan Ba Musulmin Kwarai Bane - Melaye Ya Doke Tinubu a Gasar Karanta Fatiha

Daily Trust ta ce Tsohon mataimakin shugaban kasan ya kira Peter Obi da sabon shiga kana ya zargi gwamnati mai ci ta APC da jefa yan Najeriya cikin, "halin kakanikayi."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A kalamansa, Atiku ya ce:

"Gogewa tana da amfani kuma ya zama tilas mu guje wa kuskuren da muka tafka a baya. Hadari ne babba yan Najeriya su damƙa amanar gobensu hannun sabon shiga mara gogewa ko jagoran jam'iyar da ta kawo mu cikin wannan yanayin."
"Muna cikin kakar zabe saboda haka zaku ji maganganu daga bakunan barayin mai, makaryatan manzanni, masu sayar da fatan karya da kididdiga ta wofi, duk zaku ji su, don haka ku kiyaye."
"Wajibi mu tuna ba zamu yarda da Likitan mai kara wa majinyaci guba da sunan magani, yanayi ya tsananta, ya zama tilas mu guji kuskure. Da yuwuwar wannan ce damar mu ta karshe."

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Fadi Wadanda Zai ba Mukamai da Abin da Zai Yi Kafin Kwana 100 a Aso Rock

Bugu da kari, Atiku yace yan Najeriya sun shiga matsin tattalin arziki fiye da shekarar 2015 kuma rashin ayyukan yi kullum karuwa yake a kasar nan, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

PDP zata samu galaba a shiyyoyi 4 - Saraki

A wani labarin kuma Tsohon shugaban majalisar dattawa yace jam'iyyar PDP na da babban kalubale a shiyyoyi biyu na Najeriya

Sanata Abubakar Bukola Saraki ya bayyana cewa jam'iyar Labour Party ce babbar matsalar PDP a shiyyar kudu maso gabas.

A cewar tsohon gwamnan jihar Kwara, yana da kwarin guiwar PDP zata doke manyan abokan hamayyarsa a shiyyoyi 4.

Asali: Legit.ng

Online view pixel