Jam'iyar APC Ta Rasa Kaso 70 Na Magoya Bayanta a Arewa, Jibrin

Jam'iyar APC Ta Rasa Kaso 70 Na Magoya Bayanta a Arewa, Jibrin

  • Kakakin kamfen jam'iyyar NNPP mai kayan marmari yace APC ta rasa sama da kaso 70 na masu kaunarta a arewacin Najeriya
  • Abdulmumin Jibrin yace tuni Kwankwaso ya kwace dukkanin wannan goyon baya kuma zai ci zabe ya zama shugaban kasa
  • Tsohon dan majalisar wakilan tarayyan ya bar APC ne bayan samun sabani da gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje

Abuja - Abdulmumin Jibrin, mai magana da yawun kwamitin kamfen New Nigeria Peoples Party (NNPP) ya ce APC zata sha wahala a babban zaben watan Fabrairu mai zuwa.

Jibrin ya yi wannan furucin ne yayin da yake hira da kafar Talabijin ta Channels tv ranar Litinin 9 ga watan Janairu, 2023.

Yace a yanzun duk kaunar da ake wa jam'iyya mai mulki a baya a arewacin Najeriya ya koma wurin Rabiu Kwankwaso, dan takarar shugaban kasa a inuwar NNPP.

Kara karanta wannan

Kwankwaso Ya Dauki Sabbin Alkawurra a Bangaren Ilimi, Ya Bude Shafin Tallafin Kamfen 2023

Abdulmumin Jibrin.
Jam'iyar APC Ta Rasa Kaso 70 Na Magoya Bayanta a Arewa, Jibrin Hoto: Abdulmumin Jibrin
Asali: UGC

Tsohon dan majalisar tarayya daga Kano ya kara da cewa PDP da APC na tsaka mai wuya a kan siradin rushewa, kamar yadda jaridar The Cable ta rahoto.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kakakin NNPP ya ce Kwankwaso zai lashe dukkan kuri'un Kanawa kuma ya ci zabe da nasarar raba ni da yaro, a cewarsa babu wani dan takarar shugaban kasa da zai samu kaso 25% a Kano.

Jibrin ya ce:

"Duk lokacin da APC zasu yi hasashe kan PDP suna cewa ta rasa Kwankwaso, ta rasa Peter Obi, ta rasa gwamnoni 5. Tabbas PDP na cikin rigingimu amma ba ita kadai ba APC kanta tana cikin yanayi mai kalubale da wahala."
"Kuri'u miliyan 12m da suke taƙama da su yanzu ta fece, a halin da ake ciki yanzu, jam'iyyar APC ta rasa kaso 70 zuwa 80 cikin 100 na magoya bayanta a arewacin Najeriya."

Kara karanta wannan

NNPP Ta Bayyana Abin da Kwankwaso Yake Yi da Ya Sha Gaban Atiku, Tinubu da Obi

"Idan Kwankwaso ya lakume kuri'un arewa musamman arewa maso yamma da karin wadanda zai tsakuro a kudu inda yake kara karbuwa, NNPP zata samu nasara a zabe mai zuwa."

Har watan Mayu, 2022 tsohon dan majalisar tarayyan ya kasance mamba a APC kuma darakta janar da kungiyar masoyan Bola Ahmed Tinubu.

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa Jibrin ya yanke barin APC ne bayan sabani ya shiga tsakaninsu da Abdullahi Umar Ganduje, gwamnan jihar Kano.

NNPP zata fara kamfen Kwankwaso

A wani labarin kuma Tsohon Gwamnan Kano ya kaddamar da tawagar yakin neman zaben shugaban kasa na NNPP

Mai neman zama shugaban kasa a inuwar jam'iya mai kayan daɗi, Rabiu Musa Kwankwaso, yace zai fara kamfe a jihar Bauchi ranar 12 ga watan Janairu.

Da yake kaddamar da PCC-NNPP, Kwankwaso ya roki yan Najeriya masu fatan alheri su hada hannu da shi don ceto Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262