Zaben 2023: Buhari Ya Bayyana Wani Muhimmin Dalili 1 Da Zai Sa Arewa Ta Zabi Tinubu

Zaben 2023: Buhari Ya Bayyana Wani Muhimmin Dalili 1 Da Zai Sa Arewa Ta Zabi Tinubu

  • Shugaba Buhari ya yi kira ga mutanen jihar Yobe da za su zabi dan takarar shugaban kasa na APC, Bola Tinubu, a zaben da ke tafe
  • A wurin taron yakin neman zabe a ranar Talata, 10 ga watan Janairu a Damaturu, shugaban na Najeriya ya ce Tinubu zai cigaba da ayyukan cigaba da kasa da ya fara
  • A bangare guda, Tinubu shi kuma ya gode wa Shugaban Kasar saboda halarton kamfen din kuma ya yi sabbin alkawurra ga mutanen Yobe

Damaturu, Yobe - Shugaba Muhammadu Buhari ya yi kira ga yan Najeriya da mutanen Yobe da su zabi dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, a matsayin shugaban kasa na gaba.

Sanarwar da hadimin Tinubu a bangaren watsa labarai, Tunde Rahman, ya aika wa Legit.ng ta nuna cewa shugaban kasar ya yi magana ne a filin wassani na Damaturu yayin taron kamfen din takarar shugaban kasa na APC a ranar Talata, 10 ga watan Janairu.

Kara karanta wannan

Buhari Ya Ce Ya Cika Alkawuran da Ya Dauka, Tinubu Ya Ce ba Haka Abin Yake ba

Buhari da Tinubu
Zaben 2023: Buhari Ya Bayyana Wani Muhimmin Dalili 1 Da Zai Sa Arewa Ta Zabi Tinubu. Hoto: Photo credit: @Mvnaaa
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya fadawa mazauna Yobe cewa su zabi Tinubu domin shine mutumin da zai cigaba da aikin gina Najeriya da ya fara shekaru bakwai da suka gabata.

An ambato shugaban kasar na cewa:

"Na yi wa Asiwaju rakiya zuwa nan domin in fada muku cewa ku zabe shi domin zai iya cigaba da aikin gina Najeriya."

Shirin da na ke yi wa Yobe, Tinubu ya yi sabbin alkawurra

Da ya ke magana a wurin taron, Tinubu ya yi alkawarin cewa zai yi amfani da sabon filin jirgin sama na jigilar kayayyaki don bunkasa noma idan an zabe shi.

Tsohon gwamnan na jihar Legas ya jinjinawa Shugaba Buhari saboda gina filin jirgin saman da wasu ayyuka masu kyau a kasar da ya ce hannun jari ne.

Ya kuma yaba da shugaban kasa da hukumomin tsaro bisa nasarorin da suka samu kan yaki da ta'addanci.

Kara karanta wannan

Bayar Da Ilimi Mai Nagarta Shine Zai Kawo Karshen Boko Haram A Nigeria Inji Buhari

Dan takarar shugaban kasar na APC ya ce alamar cewa an samu cigaba a harkar tsaro shi yasa shi (Tinubun) ya kwana a Yobe, daren ranar Litinin.

Tinubu ya yi magana kan shirin da ya ke yi wa Yobe game da ma'adinan kasa

A game da saka hannun jari da yawon bude ido a jihar, Tinubu ya yi alkawarin zai yi aiki tare da gwamnatin jihar don saka hannun jari da binciko ma'adinai na kasa da ke jihar.

Ya kara da cewa:

"Limestone, trona da gypsum da kuke da shi zai samarwa jihar kudin shiga. Za a inganta kasar Yobe, yashi, da wuraren da tsuntsaye ke kiwo don masu yawon bude ido."

Ya yi alkawarin zai kirkiri ayyuka ga mutanen jihar musamman matasa, yayin da zai inganta harkar ilimi.

APC ta nesanta Asiwaju da wani da ke yawo tare da shugaban Amurka

A wani rahoton, kwamitin yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, ya nesanta Asiwaju Bola Tinubu da wani hoto da ake bazawa tare da shugaba Biden na Amurka suna tattaunawa a fadar White House.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Sanatan APC Ya Bayyana Yadda Kwankwaso Da Obi Ke Yi Wa Tinubu Aiki

Bayo Onanuga, kakakin PCC ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar yana mai cewa hoton karya ce ake son jinginawa Tinubu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel