Bayar Da Ilimi Mai Nagarta Shine Zai Kawo Karshen Boko Haram A Nigeria Inji Buhari

Bayar Da Ilimi Mai Nagarta Shine Zai Kawo Karshen Boko Haram A Nigeria Inji Buhari

  • Shugaba Muhammadu Buhari ya jaddada aniyar jam'iyyar APC na samar da ilimi da tattalin arziki a fadin Nigeria
  • Shugaban Buhari ya tabbatar da bayar da ilimi shine abinda zai magance duk wata matsala da ta dabaibaye kasar nan
  • Ilimi kamar yadda hausawa ke fada shine gashirin zaman duniya, kuma shi ke kore duhun jahilci

Yobe - Shugaba Muhammadu Bauhari ya roki iyaye da masu kula da yara da su tura yaransu makaranta dan kawar da tunanin Boko Haram

Sanann shugaban ya roki yan jihar Yobe da su zabi jam'iyyar APC, a zabe mai zuwa tun daga sama har zuwa kasa. Rahotan The Punch

A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa ya fitar Mr Femi Adesina yace buhari na wannan maganar ne a wajen yakin neman zaben shugaban kasa da na gwamna da akayi a jihar yobe.

Kara karanta wannan

An samu ci gaba: Kafin ya sauka, Buhari zai kaddamar da jirage kiran Najeriya

Tinubu/Kashim
Bayar Da Ilimi Mai Nagarta Shine Zai Kawo Karshen Boko Haram A Nigeria Inji Buhari Hoto: Tinubu/Kashim SGF
Asali: Facebook

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sanarwar mai taken:

"Zabar Tinubu/Kashim shine zai baku damar samun ilimi mai nagarta, tsaro da tattalin arziki"

Jaridar Vanguard ta rawaito cewa shugaba Buhari ya jadda kudirin samar da ilimi mai inganci shine zai magance matsal-tsalun Boko Haram da suka addabi yankin arewa maso gabas.

Ni Maraya Ne!

Shugaba Buhari yace a wajen yakin neman zabe:

"Ni maraya ne, ban san mahaifinmun sosai ba, na shafe shekaru 9 a makarantar kwana sabida na samu ilimi, daga nan kuma na shiga aikin soja"
"Ina so ku jadada imaninku kuma ku yarda da ubangiji wanda shine ke yin komai, kuma in kun yarda da shi bazai juya muku baya ba"

Buhari ya roki yan takarkarin jam'iyyar APC kan in an zabe su suyi gaskiya da rikon amana, kar su watasa masa kasa a ido

Kara karanta wannan

A Gaban Buhari a Yobe, Bola Tinubu Ya Faɗi Matakin da Zai Dauka Kan ASUU Idan Ya Ci Zaben 2023

A yayin da yake batu yayin yakin neman zaben, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Bola Tinubu yace yan Nigeria suyi watsi da batun da jam'iyyun adawa ke cewa Buhari bai yi komai ba.

"Wannann gwamnatin cike take da gaskiya da rikon amana"

Tinubu yayiwa daliban Nigeria alkawarin baza su sake shafe shekaru sama da wanda aka daukar musu zasuyi a jama'ia ba sabida yajin aikin malaman jami'o'in su

Daga nan shima ya roki da yan jihar yobe da su zabi jam'iyyar APC daga sama har kasa a salon "Top to Bottom"

Wannda Suka Halarci Yakin Neman Zaben

Daga cikin wanda suka halarci yakin neman zaben sun hada da gwamnonin yankin arewa maso gabas da shugaban jam'iyyar da dan takarar mataimakin shugaban kasa da shugaban yakin neman zaben Tinubu/Kashim da dai sauransu

Asali: Legit.ng

Online view pixel