2023: Jam'iyyar APC Ta Nesanta Tinubu da Wani Dake Yawo Tare Da Shugaban Amurka

2023: Jam'iyyar APC Ta Nesanta Tinubu da Wani Dake Yawo Tare Da Shugaban Amurka

  • Jam'iyyar APC ta hannun kwamitin kamfen PCC ta karyata jita-jitar cewa Bola Tinubu ya tafi ƙasar Amurka
  • A wani Hoto dake yawo a kafafen sada zumunta, an ga Tinubu tare da Shugaba Joe Biden, amma PCC tace kagaggen hoto ne
  • Bayo Onanuga yace Tinubu na birnin tarayya Abuja kuma zai lula zuwa Bayelsa ranar Alhamis

Abuja - Kwamitin yakin neman zaɓen shugaban kasa na jam'iyyar APC (PCC) ya nesanta Bola Tinubu da wani Hoto da ake yaɗawa tare da shugaban kasar Amurka, Joe Biden suna tattaunawa a White House.

A wata sanarwa da kakakin kwamitin PCC, Bayo Onanuga, ya fitar ranar Laraba, yace Hoton shi ne na baya-bayan nan daga cikin jerin karerayin da ake jingina wa Tinubu.

Bola Ahmed Tinubu.
2023: Jam'iyyar APC Ta Nesanta Tinubu da Wani Dake Yawo Tare Da Shugaban Amurka Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Facebook

Onanuga ya bayyana cewa ɗan takarar APC yana birnin tarayya Abuja tun ranar Litinin kuma ya shirya tsaf jirginsa zai lula zuwa jihar Bayelsa ranar Alhamis.

The Nation ta ruwaito Sanarwan tace:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Wani hoto dake yawo wanda ya nuna Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da shugaban ƙasar Amurka, Joe Biden, suna tattaunawa a White House shi ne na baya-bayan nan a jerin karerayin da 'yan adawa ke kirkira."
"Kai tsaye ba zamu gane manufar wannan karya da fasadi wanda ya samo asali daga mabiyan Peter Obi. Hoton wanda aka haɗa ya bayyana ne ranar Talata da dare bayan samun labarin Tinubu zai je wasu ƙasashe."
"Duk da Amurka na ɗaya daga cikin kasashen da Tinubu zai kai ziyarsa amma muna tabbatar da cewa ɗan takararmu a Abuja ya yini ranar Talata. Yana Abuja ranar Litini kuma baya bukatar barin Najeriya kamar wasu yan takara."

Wane wuri Tinubu zai kai ziyara nan gaba?

Vanguard ta tattaro cewa yayin da yake bayanin tsare-tsaren ɗan takarar shugaban kasa na APC nan gaba, Onanuga ya ce:

"Jirgin Tinubu zai nufi jihar Bayelsa ranar Alhamis domin halartar gangamin Kamfe. A tsare-tsaren kwamitin yakin neman zaben, Tinubu ba zai bar kasar nan ba sai karshen mako."

Daga karshe kakakin PCC ya share tantamar cewa inda Tinubu zai fara zuwa bayan ya bar ƙasar na shi ne Chatham House a Landan, inda zai yi jawabi kan manufarsa ga Najeriya.

A wani labarin kuma Gwamna Wike yace nan ba da jimawa zasu zauna su yanke wanda zasu mara wa baya a zaɓen shugaban kasan 2023

Da yake kaddamar da wani Titi da gwamnatinsa ta gina, Wike ya roki mutanen jihar Ribas su zabi PDP a zaben gwamna, na yan majalisar tarayya da na majalisar jiha.

Haka zalika ya faɗa wa mutanen jihar cewa su dakace shi, nan ba da daɗewa ba zai gaya musu wanda zasu dangwala wa kuri'unsu a cikin masu neman gaje Buhari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel