Tinubu Ya Dawo da Komai Baya, Ya Fadi Gaskiyar Batun Haduwarsa da Gwamnonin PDP

Tinubu Ya Dawo da Komai Baya, Ya Fadi Gaskiyar Batun Haduwarsa da Gwamnonin PDP

  • Asiwaju Bola Tinubu ya fitar da jawabi, ya musanya cewa ya yi wata tattaunawa da ‘Yan G5 a Landan
  • ‘Dan takaran shugaban kasar ya tabbatar da ya ziyarci Landan, amma a cewarsa hanya ce ta bi da shi
  • Bola Tinubu ya ce yanzu haka yana kasar Saudi Arabia, ya yi aikin Umrah kuma yana shirin dawowa

Abuja - Asiwaju Bola Tinubu mai neman shugabancin Najeriya a 2023 a inuwar jam’iyyar APC ya karyata rahotannin da ke ta faman yawo a kan shi.

This Day ta rahoto Asiwaju Bola Tinubu yana cewa shi bai yi wani zama a boye a birnin Landan tare da Gwamnonin PDP da suka kafa kungiyar G5 ba.

A baya rahotanni sun yi ta yawo cewa ‘dan takaran na APC mai mulki ya hadu da Nyesom Wike da sauran ‘yan tawagarsa da ke fada da Iyorchia Ayu.

Kara karanta wannan

2023: Tinubu zai iya maida Najeriya ta zama sabuwa idan aka zabe shi, inji jam'iyyar APC

A wani jawabi da ya fitar ta hannun ofishin Mai magana da yawunsa, Mr. Tunde Rahman, Bola Tinubu ya ce maganar zamansa da Gwamnonin karya ne.

Zama da G5 ba gaskiya ba ne - Hadimi

A jawabin da ya yi, ‘dan siyasar ya tabbatar da cewa bai Najeriya a halin yanzu, kuma lallai ya ziyarci Landan, amma ya nuna bai zauna da gwamnonin ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu
Bola Tinubu wajen yawon kamfe Hoto: @officialasiwajubat
Asali: Facebook
“Kamar yadda ya saba idan shekara ta zo karshe, sai ya samu lokaci ya huta saboda yawon ayyukan da ke gabanshi, ya je Saudi Arabiya ya yi aikin Umrah.
Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya bi ta Landan ne a cikin mako a hanyarsa ta zuwa Makka a Saudi.
Da yake kasar Birtaniya, Tinubu ya ga wasu labarai a manyan jaridun Najeriya, ana zargin ya yi wani zaman sirri a Landan da Gwamnonin G5 da ke PDP.

Kara karanta wannan

Ganduje: Dalilin Da Yasa Arewa Ba Ta Da Wani Uzuri Sai Dai Ta Zabi Tinubu

Akalla shi ne a ce labaran nan sharri ne kuma shi aka nema. An wallafa su ne domin tattalata manufofin siyasar murabutan da masu daukar nauyinsu.

- Tunde Rahman

Abin bai dami Bola Tinubu

Vanguard ta ce ‘dan takaran shugaban kasar na zaben 2023 ya nuna wadannan labarai da sanannun wadanda ke daukar nauyinsu, sam ba su dame shi ba.

A jawabin, Tinubu ya nuna abin da ke gabansa shi ne samun nasara a zaben badi, amma ya ce babu laifi ya yi zama da wanda zai taimakawa takararsa a APC.

Sannan ‘dan takaran ya ce nan da ‘yan kwana biyu zai dawo Najeriya, ya cigaba da yawon kamfe. A karshe ya ja-kunnen masu jita-jitar nan su shafa masa lafiya.

Kalubalen da ke gaban Tinubu

A wani rahoto, kun ji cewa takarar da Asiwaju Bola Tinubu yake yi a inuwar Jam’iyyar APC mai-mulki tana fama da wasu kalubale tun daga gida.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Tinubu ya fasa kwai kan ganawa da gwamnonin G-5, ya ce akwai lauje cikin nadi

Kiristoci da-dama za su ki zaben APC saboda tikitin Musulmi-Musulmi, sannan an yi watsi da wasu jiga-jigan jam'iyyar ta APC wajen kafa kwamitin kamfe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel