Bayanin Zuwan Bola Tinubu Gidan Olusegun Obasanjo a jihar Ogun Ya Bayyana

Bayanin Zuwan Bola Tinubu Gidan Olusegun Obasanjo a jihar Ogun Ya Bayyana

  • Asiwaju Bola Tinubu ya sa labule da Olusegun Obasanjo a gidansa da ke Abeokuta a jihar Ogun
  • An samu wasu ‘Yan siyasa da suka yi wa ‘Dan takaran rakiya zuwa wajen tsohon shugaban kasar
  • Tinubu ya shaida cewa ya ziyarci Abeokuta ne domin ya gaida mutanen Ogun, ba yawon kamfe ba

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Ogun - Asiwaju Bola Tinubu mai neman zama shugaban kasa a jam’iyyar APC ya yi kus-kus da Olusegun Obasanjo a ranar Laraba, 17 ga watan Agusta 2022.

Premium Times ta rahoto cewa Asiwaju Bola Tinubu ya samu damar yi wa ‘yan jarida jawabi da ya fito daga gidan tsohon shugaban kasar a garin Abeokuta.

Asiwaju Bola Tinubu yake cewa ya ziyarci jihar Ogun ne domin ya gaida daukacin mutanen cikinta, ya kuma nuna goyon bayansa ga gwamnatin APC mai-ci.

Kara karanta wannan

Babu Baraka a NNPP: Kwankwaso Yace Shi da Shekarau Ana Tare Daram-Dam

Da ya tsaya a filin wasa na MKO Abiola, ‘Dan takaran shugaban kasar ya tunawa magoya bayansa cewa lokacin yakin neman zaben 2023 bai yi ba tukuna.

Har ila yau, an ji Tinubu yana yabawa Gwamna Dapo Abiodun da gudumuwar da mutane ke ba shi. Da alama hakan sako ne ga masu sukar gwamnatin APC.

Bola Tinubu ya tofawa Ogun albarka

“Ba a soma kamfe ba tukuna. Na dai zo ne kurum domin in gaida ku, in ce maku sannu.Allah ya yi wa Ogun albarka, Allah ya yi wa Najeriya da ‘Ya ‘yanku albarka.”

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

- Bola Tinubu

Bola Tinubu Gidan Obasanjo
Bola Tinubu a gidan Olusegun Obasanjo Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Ziyara gidan Obasanjo

Legit.ng Hausa ta fahimci Tinubu bai ce komai a kan ziyarar da ya kawowa Cif Olusegun Obasanjo ba, ya shafe kusan awa uku a gidan tsohon sojan.

Daily Post tace wadanda suka yi wa Tinubu rakiya zuwa gidan Obasanjo sun hada da Hon. Femi Gbaajabiamila, Cif Bisi Akande sai Mallam Nuhu Ribadu.

Kara karanta wannan

Rigimar Gidan PDP Ta Cabe da Fitowar Tsohon Bidiyon Shugaban Jam’iyya

Da kusan karfe 1:00 jirgin ‘dan takaran ya isa OOPL, ya samu tarba daga Gwamna Dapo Abiodun tare da Segun Osoba, Gbenga Daniel da Olakunle Oluomo.

Daga nan Tinubu suka sa labule da Obasanjo, shi kuma ‘yan tawagarsa suka hadu da Balogun Owu. Babu wanda ya san abubuwan da aka tattauna a kai.

Bayan shafe kimanin sa’a guda ana magana, Obasanjo da tsohon gwamnan na Legas sun sake shiga wani daki. Daga nan ne sai aka fito fili, aka ci abinci.

Rikicin siyasar NNPP

Mun samu labari cewa Rabi'u Musa Kwankwaso, ya ce tsakaninsa da mutanen Sanata Ibrahim Shekarau babu wata rigima kamar yadda ake fada.

‘Dan takaran shugaban kasar na NNPP ya shaidawa ‘yan jarida haka. Kwankwaso ya fadi abin da ya sa ba su iya biyawa mutanen Shekarau bukatunsa ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel