Kwankwaso Ya Kai Takararsa Zuwa Ketare, Zai Gana da Muhimman Gwamnatin Amurka

Kwankwaso Ya Kai Takararsa Zuwa Ketare, Zai Gana da Muhimman Gwamnatin Amurka

  • Rabiu Musa Kwankwaso ya isa kasar Amurka, zai tattauna a kan abin da ya shafi takarar 2023
  • ‘Dan takaran shugaban kasar zai yi zama da wasu daga cikin manyan jami’an gwamnatin Amurka
  • Kwankwaso mai takarar shugaban kasa a NNPP ya sanar da cewa za ayi taron a Washington DC

USA - Rabiu Musa Kwankwaso ya yi amfani da shafinsa na Twitter, ya shaidawa Duniya cewa jirginsa ya sauka kasar Amurka lafiya lau.

Sanata Rabiu Kwankwaso wanda yake harin kujerar shugabancin Najeriya a zaben 2023 yace zai yi zama da manyan gwamnatin kasar Amurka.

Bisa dukkan alamu a wajen taro da za ayi, ana sa ran Kwankwaso zai tattauna a kan abin da ya shafi manufofinsa da takarar 2023 da jami’an.

Kafin Kwankwaso, ‘yan takaran jam’iyyun hamayya irinsu Atiku Abubakar da Peter Obi sun je Amurka domin su shiryawa shiga takaran badi.

Kara karanta wannan

Nwankwo ya Shiga Hannun ‘Yan Sanda Bayan Shekaru 7 Ana Bibiyarsa Kan Zargin Garkuwa da Mutane

Mun isa Amurka - Kwankwaso

Na isa kasar Amurka, inda zan tattauna da wasu manyan jami’an gwamnatin kasar Amurka a birnin Washington DC. — RMK

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wani hadimin tsohon Ministan ya tabbatar da cewa tawagarsu ta isa Amurka a ranar Alhamis, amma bai yi bayanin yadda zaman zai kasance ba.

KwankwasoRM
Rabiu Musa Kwankwaso na jam’iyyar NNPP Hoto: @KwankwasoRM
Asali: Twitter

Maganar da ‘dan takaran ya yi ta jawo surutu da martani daga masu amfani da Twitter.

Me mutane suke fada a Twitter?

Wani mai suna @Kabieesi ya koka da halin mutanen Najeriya, yace babu bukatar mai neman takara ya rika ziyartar kasashen Amurka da Ingila.

"‘Yan takaranmu sun damu sosai, suna bada muhimmanci ga daukar hoto tare da shugaban kasar Amurka ko Firayim Ministan Birtaniya."

- @Kabieesi

"Ran ka ya dade, ka fada mana gaskiy; kana cikin takarar nan ko kuwa, domin duk wani mai neman shugabanci yana Najeriya, yana kamfe, amma kai kana Washington DC.

Kara karanta wannan

Ya’yan Buhari sun shiga yakin neman zaben mata na Tinubu-Shetima a Katsina

Kana can kana daukar hotuna, kai, ba ka ma soma kamfe ba, kuma zabe saura watanni uku.

- Faruk Danyaya

"Abin ya burge ni da ka ke dauke da hularka har a Amurka, amma ka da ka yarda da masu fada maka cewa kai ne shugaban kasa mai jiran-gado."

- Solomon Ayokanmi

Wani kuma yake cewa tsohon Gwmanan na Kano yana burge shi, amma ba zai zabe shi a takarar shugaban kasa ba saboda yana tare da Peter Obi.

2023 sai Bola Tinubu/Kashim Shettima

Labari ya zo cewa wasu sun yi wa Bola Tinubu/Kashim Shettima alkawarin kuri'un mutanen Jihar Kogi a Takarar Shugabancin Najeriya na 2023.

Irinsu kungiyar Team Gamji for Asiwaju/Shettima Presidency sun ce sai inda karfinsu ya kare a kan Jam’iyyar APC a yankin Okene a Kogi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel