Lema ta yage: Tsohon kwamishina a jihar Abia ya koma jam'iyyar APC
- Tsohon kwamishina a jihar Abia ya koma jam'iyyar APC
- Dakta Anthony Agbazuere ya bayyana cewa rashin kyakkyawan tsari na gudanar da jam'iyyar ta PDP ne ya sa ya bar ta
Kamar dai yadda muke samu daga majiyar mu shine tsohon kwamishinan labarai da tsare-tsare a jihar Abia Dakta Anthony Agbazuere ya sanar da ficewar sa daga jam'iyyar PDP a zuwa jam'iyya mai mulki a gwamnatin tarayya ta APC.
KU KARANTA: Wutar lantarki ta kashe wani jariri a Legas
Kamar yadda muka samu, Dakta Anthony Agbazuere ya bayyana cewa rashin kyakkyawan tsari na gudanar da jam'iyyar ta PDP ne ya sa ya bar ta.
Legit.ng ta samu cewa Mista Anthony Agbazuere ya bayyana cewa yanzu zama a jam'iyyar ta PDP ya zamar masa wani abu mai wahala musamman ma ganin yadda wasu mutanen da ya kira masu hana ruwa gudu sun shiga jam'iyyar sun kuma hana harkokin mulki gudana yadda ya kamata.
A wani labarin kuma, Shugaban jam'iyyar adawa ta PDP a kasar nan ta Najeriya mai suna Uche Secondus ya bayyana a jiya Laraba cewar shi fa tare da jam'iyyar sa ta PDP ba za su taba bari ayi magudin zabe ba a shekarar 2019 mai zuwa.
Mista Secondus ya bayyana hakan ne a yayin da jagoranci sauran wasu 'yan kwamitin gudanarwar jam'iyyar da sauran wasu masu ruwa da tsaki zuwa garin Yenagoa, babban birnin jihar Bayelsa domin taya gwamnan murnar shekara 6 bisa karagar mulki.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng