‘Yan Tinubu Sun Ambaci Jihar Arewa 1 da Za Tayi Wa Atiku Nisa, APC Za Tayi Galaba

‘Yan Tinubu Sun Ambaci Jihar Arewa 1 da Za Tayi Wa Atiku Nisa, APC Za Tayi Galaba

  • ‘Yan kungiyar Team Gamji for Asiwaju/Shettima Presidency za su taimakawa jam’iyyar APC a 2023
  • Shugaban kungiyar magoya bayan, Alhaji Sanusi Abubakar ya sha alwashin taimakawa Bola Tinubu
  • An yi wa Bola Tinubu alkawarin samun kuri’un mutanen yankin Kogi ta tsakiya a Arewacin Najeriya

Kogi - ‘Yan tafiyar Team Gamji for Asiwaju/Shettima da suke goyon bayan takarar Bola Tinubu a zaben 2023, sun hango nasara a 2023.

Daily Trust ta kawo rahoto a ranar Alhamis, 1 ga watan Disamba 2022, a nan aka ji cewa an yi wa Bola Tinubu alkawarin lashe zaben yankin Kogi.

Shugaban Team Gamji for Asiwaju/Shettima Presidency a Najeriya, Alhaji Sanusi Abubakar ya yi alkawarin za su ba jam’iyyar APC goyon baya.

Sanusi Abubakar ya nuna cewa za suyi duk abin da ya dace wajen ganin Asiwaju Bola Tinubu da Kashim Shettima sun dare kan karagar mulki.

Kara karanta wannan

2023: APC Ta Nesanta Tinubu da Wani Hoto da Ake Yaɗawa Tare da Shugaban Amurka, Ta Faɗi Gaskiya

Za a zabi APC a Kogi ta tsakiya

Kamar yadda shugaban wannan kungiya ya fada, za a tattaro mutanen yankin Kogi ta tsakiya su zabi ‘yan takaran da APC mai rike da mulki ta tsaida.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Rahoton yace ‘dan siyasar ya yi wannan kira ne a lokacin da ya kai wata ziyara ta musamman domin samun goyon bayan al’ummar da ke jihar Kogi.

Bola Tinubu
Bola Tinubu yana kamfe Hoto: @officialasiwajubat
Asali: Facebook

Dalilin Abubukar na goyon bayan ‘dan takaran shi ne ya taka rawar gani wajen ganin an dawo da mulkin farar hula a Najeriya a karshen shekarar 1998.

Yawan mutane su ne kasuwa

Shi kuma Alhaji Kent Abubakar wanda shi ne shugaban kungiyar Team Gamji, ya tabbatar da cewa za su taya APC yakin neman cin zabe a 2023.

Alhaji Kent Abubakar yake cewa siyasa sai da jama’a, kuma daga gida ake fara samun nasara, don haka suna da mutanen da za su a lashe zabe.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Jaruman Super Eagles Za Su Kaddamar Da Kamfe Din Tinubu A Kano

Tattaki a Okene

Hakan na zuwa ‘yan kwanaki bayan Tribune ta rahoto ‘yan kungiyar Team Gamji sun shirya tattakin mutum miliyan daya domin nuna goyon bayan APC.

An faro wannan tattaki na musamman ne daga filin Inike a karamar hukumar Okene. Taron ya jawo mutane daga garuruwa biyar na tsakiyar jihar Kogi.

Rikicin NNPP a Kaduna

Labari ya zo a baya cewa a reshen jihar Kaduna, wasu ‘yan jam’iyyar adawa ta NNPP sun koka da takarar Gwamnan Suleiman Othman Hunkuyi a 2023.

Abubuwa ba su tafiya daidai a jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) mai alamar kayan dadi, suna so a canza wanda zai yi takarar Gwamna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel