'Tinubu Ya Kere Sauran Yan Takara Damar Lashe Zaben Shugaban Kasa a 2023'

'Tinubu Ya Kere Sauran Yan Takara Damar Lashe Zaben Shugaban Kasa a 2023'

  • Shugaban kwamitin yakin neman zaɓen shugaban kasa na APC a ƙasar Kanada ya yi hasashen Bola Tinubu ne zai lashe zaɓen 2023
  • Barista Jide Oladejo, yace Tinubu ne ɗan takara ɗaya tilo daga rukunin masu son gaje Buhari da ya gina tubalin nasara
  • Ya kuma yaba da kokarin gwamnati na kafa hukumar mazauna kasar waje amma yace suna jiran a fara basu damar kaɗa kuri'a

Akure, Ondo - Shugaban kwamitin yakin neman zaben shugaban ƙasa na jam'iyyar APC reshen ƙasar Kanada, Barista Jide Oladejo, yace damar Asiwaju Bola Tinubu na lashe zaben 2023 ta kere na sauran haske.

Jaridar The Nation ta ruwaito Oladejo na cewa Tinubu ya riga da ya gama duk wani shiri na zama shugaban kasa na gaba a Najeriya.

Bola Ahmed Tinubu.
'Tinubu Ya Kere Sauran Yan Takara Damar Lashe Zaben Shugaban Kasa a 2023' Hoto: Bola Tinubu
Asali: UGC

Mista Oladejo, wanda ya zanta da manema labarai a Akure, yace Tinubu ya fita daban daga cikin masu hangen kujera lamba ɗaya, ɗan siyasar zamani wanda ya shirya inganta walwalar 'yan Najeriya.

Yace jam'iyyar APC a ƙasar Kanada zata wayar da kai kan kudirin Bola Tinubu domin tabbatar da ya samu nasarar raba ni da yaro a zaɓe mai zuwa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A jawabinsa, Oladejo ya ce:

"Najeriya ƙasa ce mai ban sha'awa domin kowane ɗan kasa burinsa ya ɗare kan muƙamin shugabanci ba don komai sai don su yi wadaƙa da dukiyar al'umma."
"Sanata Tinubu na daban ne ɗan takara ne mai goshin nasara, zai lashe zaɓen shugaban ƙasa dake tafe don haka damarsa ta lashe zabe ta fi haske kan saura."
"Shi ne mutum ɗaya tilo daga cikin yan takara da ya kasance ɗan siyasar zamani, wanda ya haɗa kan kowa ya lashe tikitin APC kuma a shirye yake ya ƙara inganta rayuwar 'yan Najeriya."

Oladejo ya yaba da kafa hukumar 'yan Najeriya mazauna ƙasashen waje amma yace alfanunta na gaske ba zai cika ba sai an fara basu dama su kaɗa kuri'unsu a zaɓe.

Matasan Katsina Sun Yi Wa Atiku Alkawarin Kuri'u Miliyan Shida a Zaben 2023

A wani labarin kuma Matan jihar Katsina sun sha alwashin yin duk me yuwuwa wajen haɗawa dan takarar PDP kuri'u miliyan 6m a zaɓen 2023

Matasa karkashin kungiyar Atiku Support Organization sun bayyana shirin da suke wa ɗan takarar shugaban kasa a PDP, Atiku Abubakar a jihar Katsina.

Kodinetan ƙungiyar, Yasir Ibrahim, ne ya bayyana haka yayin rantsar da Kodinetocin kananan hukumomi 34 dake faɗin jihar, waɗan zasu yi aiki don cika alƙawarin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel