Gwamnan APC Ya Nemi Gwamna Wike Ya Baiwa Tinubu Kuri'un Mutanen Ribas a 2023

Gwamnan APC Ya Nemi Gwamna Wike Ya Baiwa Tinubu Kuri'un Mutanen Ribas a 2023

  • Gwamnan Jihar Ebonyi yace ɗan takarar shugaban kasa na APC baya bukatar taimakon kayan yakin neman zaɓen daga Wike
  • Dave Umahi, lokacin kaddamar da wani aiki a Ribas, yace abinda Tinubu ke bukata daga Wike shi ne kuri'un mutanen jiharsa
  • Wike wanda yake takun saƙa da tsagin Atiku a PDP, ya ɗauki alƙawarin taimaka wa Obi da Kwankwaso

Rivers - Gwamna Dave Umahi na jihar Ebonyi yace ɗan takarar shugaban kasa a inuwar APC, Bola Tinubu, ba ya bukatar tallafin kayan kamfe daga gwamnan Ribas, Nyesom Wike.

Channels tv ta rahoto Umahi na cewa maimakon haka, Tinubu na buƙatar kuri'un mutane jihar mai tarin albarkatun man Fetur.

Gwamna Umahi da Wike.
Gwamnan APC Ya Nemi Gwamna Wike Ya Baiwa Tinubu Kuri'un Mutanen Ribas a 2023 Hoto: Rivers State Ministry of Works
Asali: Facebook

Gwamna Umahi na jam'iyyar APC, ɗaya daga cikin jagororin yakin neman zaɓen Tinubu a kudu maso gabas, ya faɗi haka ne ranar Talata lokacin da ya kaddamar da Titin Akpabu-Itu-Umudiogha.

Tun farko, Gwaman Wike ne ya gayyaci takwaransa na jihar Ebonyi domin ya kaddamar da aikin Titin da aka kammala a yankin ƙaramar hukumar Emohua, jihar Ribas.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Kana da kokarin ɗaukar alƙawari," Umahi ya faɗa wa Wike.

"Idan kace zaka ba da tallafin kayan aiki na san zaka cika amma a jam'iyyar APC bamu bukatar taimakon kayayyakin aiki, kuri'u muke so, na zaɓen shugaban kasa kaɗai dan Allah."
"Abinda nake rokonka kawai na zaɓen shugaban kasa kaɗai, batun zaɓen kujera lamba ɗaya kabarwa Asiwaju kuma Asiwaju zai zo nan da kansa neman kuri'u."

Wike, wanda ba ya ga maciji da ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyarsa PDP, Atiku Abubakar, ya yi wa masu hangen kujerar Buhari biyu alƙawarin kayan kamfe a jiharsa, Vanguard ta ruwaito.

Legit.ng Hausa ta gano cewa waɗanda gwamnan ya ɗaukar wa alƙawarin sune, Rabiu Musa Kwankwaso na jam'iyyar NNPP da Peter Obi na Labour Party.

Kwankwaso Ya Tsoma Baki a Rikicin Wike da Atiku, Ya Fadi Wanda Ke Kan Gaskiya

A wani labarin kuma mai neman gaje kujerar Buhari karkashin NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso ya yi tsokaci kan rigingimun da suka dami PDP

Yayin kaddamar da wasu ayyuka a jihar Ribas, Tsohon gwamnan Kano yace tsagin G5 na tafiyar da harkokin gunin sha'awa kuma kan gaskiya.

A cewarsa, ɓangaren tawagar gaskiya da ya ƙunshi wasu gwamnonin PDP karkashin Wike sun san abinda suke yi, suna neman shawari da zaman tattauna wa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel