Dirama Yayin da Wasu Mambobin PDP Suka Share Filin da APC Ta Gudanar da Gangamin Kamfe a Jos

Dirama Yayin da Wasu Mambobin PDP Suka Share Filin da APC Ta Gudanar da Gangamin Kamfe a Jos

  • Magoya bayan babbar jam'iyyar adawa ta PDP sun kai ziyara filin wasan Rwang Pam inda APC ta kaddamar da yakin neman zaben shugaban kasa
  • Matasan da suka isa wajen a ranar Laraba, 16 ga watan Nuwamba sun share tare da wanke wurin tsaf
  • A cewarsu sun yi hakan ne domin kawar da duk wasu abubuwa da jam'iyya mai mulki ta shigo da shi jihar

Plateau - Mazauna garin Jos musamman matasa da ke goyon bayan jam'iyyar PDP sun yi tururuwan zuwa filin wasa na Rwang Pam, inda APC ta kaddamar da yakin neman zabenta don yiwa wajen wankan tsarki a ranar Laraba.

Wannan mataki da suka dauka na zuwa ne kasa da sa'o'i 24 bayan jam'iyyar APC mai mulki ta kaddamar da kamfen dinta na shugaban kasa a babban birnin jihar Plateau, jaridar Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan

Karin haske: Majalisa ta amince a sake fasalin Naira, amma ta tono wani batu mai girma

Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ta rahoto cewa kungiyoyin da ke goyon bayan PDP da dama da suka hade da matasan, sun ce sun yi hakan ne don nuna jajircewarsu na son fatattakar APC daga Plateau a zabe mai zuwa.

An yi wankin inda su Tinubu suka taka a Jos
Dirama Yayin da Wasu Mambobin PDP Suka Share Filin da APC Ta Gudanar da Gangamin Kamfe a Jos | Hoto: pulse.ng
Asali: UGC

Kamru Sani, darakta janar na kungiyar Atiku Motivational Movement, wanda ya bayyana hakan ya ce sun aikata abun da suka yi ne don share abubuwan da APC ta kawo jihar.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Jos gari ne na PDP, inji wanda ya jagoranci wanke inda su Tinubu suka taka

Sani ya bayyana cewa plateau jihar PDP ce kuma a shirye take ta koma ga matakan nasararta.

Ya ce:

"Mun zo nan ne don share duk abubuwan da suka kawo nan, domin PDP ita ce ta Plateau da Najeriya.
"Jam'iyyar ta shirya sake bin hanyoyin nasara, domin ta nuna cewa ita din ce jam'iyyar gaskiya ga jihar.

Kara karanta wannan

Kicibus: Bidiyon yadda Tinubu da Atiku suka yi gamuwar ba zata a filin jirgin sama

"Jam'iyyar zata kawo sauki ga wannan wahala da al'ummar jihar da Najeriya ke fama da shi tsawon shekaru bakwai da suka gabata."

Da yake jawabi, Mohammed Hassan, shugaban matasan PDP, ya ce wannan tafiya zata kare makomar matasa a Najeriya, rahoton Daily Trust.

Hassan ya ce yan Najeriya shaidu ne ga irin shugabancin da aka dandana a shekaru bakwai da suka gabata, sannan ya yi kira ga yan Najeriya da su zabi PDP a 2023.

Tinubu ya caccaki su Peter Obi da Atiku

A taron na Jos, Tinubu ya caccaki dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar da kuma na jam'iyyar LP, Peter Obi.

Tinubu ya ce dukkansu basu dauko hanyar gaskiya ba, don haka basu cancanci kuri'un 'yan Najeriya ba a zaben 2023.

'Yan siyasa na ci gaba da ruwan kalamai masu zafi yayin da aka fara kamfen zaben 2023 mai zuwa badi.

Kara karanta wannan

Tsagerun 'Yan Bindiga Sun Bindige Dan Sa-kai Da Wasu Mutane 4 a Wata Jahar Arewa

Asali: Legit.ng

Online view pixel