Fitattun Jagororin Jam'iyyar PDP Sun Koma APC A Jihohin Sokoto da Zamfara

Fitattun Jagororin Jam'iyyar PDP Sun Koma APC A Jihohin Sokoto da Zamfara

  • Jam'iyyar adawa ta PDP ta yi rashin wasu manyan jiga-jiganta a jihohin Zamfara da Sokoto da ke Arewa maso Yammacin Najeriya
  • A jihar Sokoto, Alhaji Sahabi Bojo-Bodinga ne ya sauya sheka tare da magoya bayansa zuwa jam'iyyar APC
  • Tsohuwar shugabar mata a PDP, Hajiya Madina Shehu ta saki jam'iyyar PDP, ta kama tallan tsintsiyar APC

Jihar Sokoto - Alhaji Sahabi Bojo-Bodinga, fitaccen jigon jam'iyyar PDP a jihar Sokoto ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC tare da dimbin magoya bayansa.

Sahabi ya samu tarba ne zuwa APC daga babban mai tafiyar da ita a jihar Sokoto, Sanata Aliyu Wammako a gidansa da ke Sokoto a ranar Juma'a 4 ga watan Nuwamba, The Nation ta ruwaito.

Jiga-jigan PDP sun yi kaura zuwa APC a jihohin Sokoto da Zamfara
Fitattun Jagororin jam'iyyar PDP Sun Koma APC A Jihohin Sokoto da Zamfara | Hoto: @Bellotsoho
Asali: Twitter

APC ta samu babban ci gaba, inji hadimin sanata Wammako

Kara karanta wannan

2023: APC ta Tarbi Fiye Da Mutum 1000 Da Suka Sauya Sheka Daga PDP A Zamfara

Hadimin Wammako a harkokin yada labarai, Bashar Abubakar ya bayyana shigowar Sahabi APC a matsayin nasara da karin ci gaba ga jam'iyyar a zaben 2023 mai zuwa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Bashar ya bayyana cewa, Alhaji Isa Sadiq-Achida, shugaban APC ya tabbatarwa sabbin mambobin da magoyansu samun duk wata kulawa kamar yadda ake ba tsoffin mambobi.

Shugabar Matan PDP Ta Zamfara Madina Shehu Ta Koma APC Mai Mulki

Madina Shehu, shugabar mata ta jam'iyyar PDP a jihar Zamfara ta bayyana sauya sheka zuwa jam'iyyar APC mai mulki a jihar.

Madina ta bayyana sauya shekarta ne a ranar Alhamis 3 ga watan Nuwamba a birnin Gusau bayan ganawa da gwamna Mawatalle na jihar Zamfara.

Ta bayyana dalilin komawarta APC da cewa, sam babu shugabanci nagari a jam'iyyar PDP, kamar yadda TheCable ta ruwaito.

Kara karanta wannan

2023: APC Ta Yi Babban Kamu A Sokoto Yayin Da Dattijon Jigon PDP Da Mutanensa Suka Sauya Sheka

A cewarta:

"Na ayyana sauya sheka zuwa APC tare da shugabannin mata na kananan hukumomi 14 na jihar."

Akwai Yuwuwar ’Yan Siyasa Su Yi Amfani Da ’Yan Daba Wajen Gangamin Kamfen Zaben 2023, Inji DSS

A wani labarin kuma, hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta gargadin cewa, akwai yiwuwar 'yan siyasa a kasar nan su yi amfani da tsagerun 'yan daba a gangamin su na zaben 2023, Daily Trust ta ruwaito.

Wannan na fitowa ne daga bakin daraktan DSS a Kaduna, Mr Abdul Enachie yayin gabatar da rahotonsa kan tsaro a jihar ta Kaduna.

Ya bayyana cewa, akwai bukatar gwamnati ta mai da hankali sosai tare da wayar da kan matasa don gudun amfani dasu wajen aikata barna a fadin kasar nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel