Yanzu Yanzu: Tsohon Sakataren Gwamnatin Katsina, Mustapha Inuwa, Ya Sauya Sheka Daga APC Zuwa PDP

Yanzu Yanzu: Tsohon Sakataren Gwamnatin Katsina, Mustapha Inuwa, Ya Sauya Sheka Daga APC Zuwa PDP

  • Gabannin zaben 2023, tsohon sakataren gwamnatin jihar Katsina, Dr Mistapha Muhammad Inuwa, ya fice daga jam'iyyar APC
  • Inuwa wanda shine sakataren gwamnati mafi dadewa a jihar ya koma jam'iyyar PDP mai adawa
  • Kafin sauya shekarsa, ya nemi takarar tikitin gwamnan jihar karkashin jam'iyya mai mulki amma ya sha kaye a zaben fidda gwani

Katsina - Tsohon sakataren gwamnatin jihar Katsina karkashin gwanna Amiju Bello Masari mai ci, Dr Mistapha Muhammad Inuwa ya sauya sheka daga jam'iyyar All Progressives Party zuwa Peoples Democratic Party, PDP.

Dan siyasar ya kuma kasance tsohon kwamishinan ilimi a jihar.

Kara karanta wannan

Zamfara: Gwamna Matawalle Ya Rufe Gidajen Talabijin da Rediyo Saboda Rashin Da'a

Inuwa wanda shine sakataren gwamnati mafi dadewa a jihar ya sanar da sauya shekarsa a ofishin kamfen dinsa a ranar Lahadi, 16 ga watan Oktoba, Leadership ta rahoto.

Mustapha Inuwa
Yanzu Yanzu: Tsohon Sakataren Gwamnatin Katsina, Mustapha Inuwa, Ya Sauya Sheka Daga APC Zuwa PDP Hoto: Leadership
Asali: UGC

Hakan na zuwa ne bayan ya gana da daruruwan magoya bayansa da kungiyoyi wadanda suka dunga wakokin goyon bayansa a matsayin wanda zai gyara al'amuran siyasa a jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jaridar Leadership ta rahoto cewa Inuwa ya yi murabus daga matsayin sakataren gwamnati watanni da suka gabata domin takarar kujerar gwamna karkashin APC inda ya sha kaye a zaben fidda gwanin jam'iyyar.

Kara karanta wannan

Kano: Mun Shriya Tsaf Don Yiwa Kwankwaso da Ganduje Ritayar Dole a Siyasa, ‘Dan Takarar Gwamna a LP

Umar Dikko Radda ne yayi nasarar lashe tikitin jam'iyyar mai mulki. Ya yi alkawarin marawa Radda baya kafin wannan sabon ci gaban na ficewarsa daga jam'iyyar.

Atiku: Yan Arewa Na Bukatar Dan Arewa Ya Zama Shugaban Kasa Ba Bayarabe Ko Inyamuri Ba

A wani labarin, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar, ya bayyana cewa yan arewa na bukatar wani shugaban kasa da ya fito daga yankin arewacin kasar.

Atiku ya bayyana hakan ne a ranar Asabar, 15 ga watan Oktoba, a wani taron yan arewa da aka gudanar a jihar Kaduna, The Cable ta rahoto.

Yayin da yake jawabi ga taron al’ummar Hausa Fulani da dama, tsohon mataimakin shugaban kasar ya bayyana cewa basa bukatar dan Igbo ko bayarabe a matsayin shugaban kasa sai dai wani daga arewa.

Kara karanta wannan

Mazaunin Gidan Haya Ya Sace Mai Gidan Tare da Karɓar Naira Miliyan 1

Asali: Legit.ng

Online view pixel