Yadda Dan Kwallon Najeriya Ya Nutse Bayan Ceto Fasinjojin 5 A Hatsarin Jirgin Ruwa Da Ya Ritsa Da Su

Yadda Dan Kwallon Najeriya Ya Nutse Bayan Ceto Fasinjojin 5 A Hatsarin Jirgin Ruwa Da Ya Ritsa Da Su

  • Dan kwallon kafa a Bayelsa, Earnest Peremobowei, ya riga mu gidan gaskiya sakamakon nutsewa da ya yi cikin ruwa bayan ya ceto wasu mutane guda biyar
  • Rahotanni sun nuna cewa marigayin dan shekara 31 yana kan hanyarsa ne na zuwa Yenebelebiri tare da wasu mutane biyar don zuwa su duba gidajensu da ambakiyar ruwa ta cinye amma jirgin ya yi hatsari
  • Earnest Kombaye, kanin marigayin ya yi kira ga gwamnati ta tallafawa mata da yayan marigayin da iyalansa bayan ya tabbatar da rasuwar yayansa wanda ya ce abin bakin ciki ne

Bayelsa - Earnest Peremobowei, dan kwallon kafa, dan shekara 31 a nutse a Yenebelebiri a karamar hukumar Yenagoa bayan ceto mutane biyar da hatsarin jirgin ya ritsa da su.

An gano gawar dan kwallon kwana biyu bayan hatsarin an kuma kai shi Cibiyar Lafiya ta Tarayya da ke Yenagoa.

Kara karanta wannan

Goodluck Jonathan Ya Zama Dan Gudun Hijira, In Ji Gwamnan Bayelsa

Dan kwallo
Dan Kwallon Najeriya Ya Nutse Bayan Ceto Fasinjojin 5 A Hatsarin Jirgin Ruwa Da Ya Ritsa Da Su. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Daily Trust ta tattaro cewa lamarin ya faru ne a ranar Laraba da yamma lokacin da jirgin ruwa da suke amfani da shi don zuwa garinsu ya kife saboda karfin ruwa.

Marigayin ya lashe lambobin yabo masu yawa a gasa daban-daban na jihar ciki har da Internal Grace Football Club inda ya zama zakari a gasar kofin gwamnan jihar mai suna 'Prosperity Cup'.

Mazauna yankin sun fada wa yan jarida cewa yana hanyarsa ne na zuwa Yenebelebiri da ke Yenagoa, babban birnin jihar, tare da wasu mutane biyar lokacin da jirgin ya yi hadari.

Kanin marigayin ya magantu kan yadda abin ya faru

Kanin marigayin, Earnest Kombaye, wanda ya tabbatar da lamarin ya ce wanda abin ya faru da shi ya gaji ne bayan ceto mutane biyar da ke jirgin.

Kara karanta wannan

Kamfen 2023: Tinubu ya yi magana mai girma game da bashin da ake bin Najeriya

Ya ce:

"Yana tare da wasu mutane biyar wadanda ke kokarin tsallaka wa zuwa Yenebelebiri don duba yanayin ruwa da ya yi ambaliya a gidajensu.
"Amma saboda karfin ruwan, jirgin ta kwace wa direban ya bugi Government Jetty Barge. Shi kadai ne ya iya ninkaya a cikinsu sosai don haka ya ceto mutanen biyar da ke tare da shi. Ina tunanin ya gaji kuma ruwan ta tafi da shi."

An yi kira ga gwamnati ta tallafawa iyalan mammacin

Ya kuma tabbatar cewa mutum na karshe da mammacin ya ceto yana Cibiyar Lafiya ta Tarayya a Yenagoa.

Ya ce mutuwar dan uwansa abin ciwo ne, ya bayyana shi a matsayin babban rashi ga iyalin su.

Ya kara da cewa marigayin dan kwallon ya bar mata da yaya biyu mai shekara 10 da 3.

Ya yi kira ga gwamnati ta tallafawa iyalan mammacin da yayansa.

Wani Dan Wasa a Najeriya Ya Yanke Jiki Ya Fadi, Ya Mutu Ana Tsaka da Buga Kwallo

Kara karanta wannan

Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa Ya Angwance Da Gwanar Al-Qur'ani Hafiza Haulatu

A wani rahoton, wani matashi mai shekaru 31 ya yanke jiki ya fadi matacce yayin da yake tsaka da buga kwallo a yankin Lekki na jihar Lagas.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa wannan mummunan al’amarin ya afku ne a ranar Lahadi, 2 ga watan Oktoba.

An tattaro cewa matashin wanda ba a tabbatar da sunansa ba yana bin kwallo ne lokacin da ya yanke jiki ya fadi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel