2023: Mata Zasu Samu Manyan Mukamai a Gwamnatina Idan Na Gaji Buhari, Dan Takarar SDP

2023: Mata Zasu Samu Manyan Mukamai a Gwamnatina Idan Na Gaji Buhari, Dan Takarar SDP

  • Mai neman zama shugaban kasa a inuwar SDP, Mista Adebayo, yace mata na da muhimmiyar rawar da zasu taka a gwamna
  • Adewole Adebayo, yace idan har Allah ya ba ahi mulki zai ba mata manyan mukamai domin zasu taimaka
  • Adebayi ya faɗi haka ne a wurin wani taron kwana uku da ƙungiyar mata masu son shugabanci nagari suka shirya a Abuja

Abuja - Adewole Adebayo, ɗan takarar shugaban ƙasa a karkashin inuwar jam'iyyar SDP yace zai ba mata manyan kujerun siyasa idan ya zama shugaban kasa a zaɓen 2023.

A ruwayar NAN, Adebayo ya faɗi haka ne a wurin taron kwana uku da ƙungiyar mata masu muradin shugabanci nagari suka shirya a babban birnin tarayya Abuja.

Adewole Adebayo.
2023: Mata Zasu Samu Manyan Mukamai a Gwamnatina Idan Na Gaji Buhari, Dan Takarar SDP Hoto: thecable
Asali: UGC

Jaridar The Cable tace yayin da yake jawabi kan batun da aka ware don tattauna wa a taron mai taken, "Shugabanci nagari a Najeriya," ɗan takarar yace sauraron mata zai taimaka wajen warware matsalolin Najeriya.

Kara karanta wannan

Gwamnati Ta Fito Ta Fadawa Kotu Asalin Dalilin Cigaba da Tsare Nnamadi Kanu

"Ya kamata gwamnati ta zama tamkar matar gida, idan har kuna son gwamnatin da zata wa Najeriya aiki, to sai kuma canza tsarinta zuwa na matar aure a gida."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Daga nan gwamnati zata wayi gari da tunanin yadda mutane zasu ci abinci su ƙoshi kana su tafi makaranta," inji Adebayo.

Mata na da muhimmiyar rawar da zasu taka - Adebayo

A jawabinsa, Mista Adebayo dake yunkurin kwace mulki daga hannun jam'iyyar APC a zaɓen 2023, yace:

"A iya abinda na fuskanci gwamnati, mata na da rawar da zasu taka saboda na taso cikin kulawa mai kyau. A takaice na samu dabi'ar son shugabanci ne daga yadda aka raine ni."
"Matsalolin gwamnati ba su shafe ni ba sosai saboda gidan da aka raine ni. Saboda haka matukar zan hau kan gadon mulki ko gwamnati, na tsawon lokaci ko gajere zan tallafa wa iyalai domin nan ne tushen matsalar Najeriya."

Kara karanta wannan

2023: Saura Kiris Na Zama Shugaban Kasa, Bola Tinubu Ya Gana da Malaman Tijjaniyya a Kano

A wani labarin kuma na daban kuma An Bukaci Gwamnan Jihar Edo, Godwin Obaseki, Ya Yi Murabus

Babbar jam'iyyar hamayya a jihar Edo, watau APC ta yi kira ga gwamnan jihar, Godwin Obaseki, ya yi murabus nan take.

Wannan kira na zuwa ne bayan gwamna Obaseki yace gwamnatinsa zata samu koma baya sakamakon maida hankali kan harkokin kamfe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel