Gwamnati Ta Fito Ta Fadawa Kotu Asalin Dalilin Cigaba da Tsare Nnamadi Kanu

Gwamnati Ta Fito Ta Fadawa Kotu Asalin Dalilin Cigaba da Tsare Nnamadi Kanu

  • Ministan shari’a ya yi wa kotu bayanin abin da ya sa gwamnati ba ta da niyyar sakin Mazi Nnamdi Kanu
  • Wani ma’aikaci a OAGF yace barin Nnamadi Kanu ya samu ‘yanci zai haddasa rashin zaman lafiya a kasa
  • Amma Lauyan da ya tsayawa Kanu, ya musanya zargin nan, yace fito da shugaban IPOB ne zaman lafiya

Abuja - Gwamnatin Tarayya ta bada dalilanta na cigaba da rike Nnamadi Kanu alhali wani Alkali kotun daukaka kara ya yanke hukunci cewa a fito da shi.

Vanguard ta rahoto gwamnatin Najeriya tana bayanin abin da ya sa har yanzu shugaban kungiyar IPOB watau Nnamadi Kanu yake hannun hukuma.

A wata takarda da ta aikawa kotu a ranar Litinin, gwamnatin tarayya tace fito da Kanu yana da hadari domin shi barazana ne ga lamarin tsaron kasa.

Kara karanta wannan

2023: Tinubu ya fadi babban sauyin da zai kawo a aikin 'yan sanda idan ya gaji Buhari

Gwamnati ta kafa hujja da shari’ar da aka yi tsakanin gwamnatin tarayyar Najeriya da Asari Dokubo, inda aka take hakkin mutum saboda a zauna lafiya.

Kamar yadda aka rahoto, Lauyan gwamnatin tarayya yace idan har hakkin wani mutum shi kadai zai tozarta sha’anin tsaro, to za a iya taka hakkinsa.

“Daga cikin hujjojinmu shi ne wannan kara ya shafi lamarin tsaron kasa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

'Dan IPOB
Wani mai goyon bayan IPOB Hoto: Naija PR
Asali: UGC

“Mun dogara da shari’ar FRN Vs Dokubo, inda kotun koli tace idan mutum ya zama barazana ga tsaro, ana ajiye maganar hakkin Bil Adama.
“Da zarar akwai barazana ta fuskar tsaro, za a dakata da batun hakkin wani mutum har sai an magance wannan barazanar tsaron tukuna.

- David Kaswe

Babban jami’in ofishin Ministan shari’a kuma babban lauyan gwamnatin tarayya, David Kaswe ya kafa hujja da wannan a madadin gwamnatin Najeriya.

Kara karanta wannan

Dalilin Na Yasa Muka Nemi Afuwar Yan Najeriya Kan Yadda Muka Gudanar Da Mulki, Aisha Buhari

David Kaswe ya kara da cewa sun samu bayanin da ke nuna fito da Kanu zai jawo lamarin tsaro a yankin Kudu maso gabashin Najeriya ya kara tabarbarewa.

Zaman lafiya shi ne Kanu ya fito

Amma Lauyan da yake kare jagoran na IPOB mai rajin kafa kasar Biyafara, Mike Ozekhome SAN yace sakin Kanu ne zai kawo zaman lafiya a fadin kasar nan.

Ozekhome SAN yace murnar da aka yi da jin hukuncin kotu zai tabbatar da hakan.

Dalilin karbar lambar girma

An ji labari Ignatius Ayau Kaigama bai karbi shawarar da mutane suka ba shi da aka ce za a ba shi lambar girma ba, ya yi watsi da masu neman a ba gwamnati kunya.

Akwai wadanda suka hurowa Limamin Katolikan wuta ya watsawa gwamnatin tarayya kasa a idanu, Faston ya soki gurguwar shawarar, ya karbi lambar girman.

Asali: Legit.ng

Online view pixel