Uwar Gidan Osinbajo Na Cikin Tawagar Yakin Neman Zaben Tinubu-Shettima, Inji APC

Uwar Gidan Osinbajo Na Cikin Tawagar Yakin Neman Zaben Tinubu-Shettima, Inji APC

  • Majiya ta naqalto cewa, uwar gidan mataimakin shugaban kasa, Dolapo Osinbajo na daga cikin masu tallata Tinubu
  • Ana ta yada jita-jitar cewa, Osinbajo da uwar gidansa ba sa cikin wadannan ke kamfen din neman nasarar Tinubu da Shettima
  • A jiya ne aka kaddamar da kwamitin gangamin kamfen din takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC mai mulki

FCT, Abuja - Jam'iyyar APC mai mulki ta bayyana cewa, cire sunan uwar gidan mataimakin shugaban kasa, Mrs Dolapo Osinbajo daga jerin tawagar gangamin kamfen din yada dan takara Bola Tinubu ba ya nufin bata ciki.

A ranar 1 ga watan Oktoba ne jam'iyyar APC ta bayyana tawagar mata daga majalisar kamfen dinta, wadda uwar gidan shugaban kasa, Aisha Buhari, uwar gidan Tinubu; Sanata Oluremi Tinubu da uwar gidan Shettima, Hajiya Nana Shettima za su jagoranta.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Buhari Ya Sha Alwashin Yi wa Tinubu Gagarumin Kamfen

Dolapo Osinbajo na ba d gudunmawa a tafiyar Tinubu
Uwar Gidan Osinbajo Na Cikin Tawagar Yakin Neman Zaben Tinubu-Shettima, Inji APC | Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Tawagar ta kamfe dai na dauke da sunayen jiga-jigan matan APC a kasar nan sama da 944, kuma uwar gidan Buhari ce uwar tawagar, amma babu sunan uwargidan mataimakin shugaban kasa, Mrs Dolapo.

Idan baku manta ba, babu sunan mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo da sakataren gidan gwamnati, Boss Mustapha a jerin tawagar kamfen din Tinubu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan kuwa ya faru ne daidai da umarnin shugaban kasa na cewa, a bar Osinbajo da Mustapha su tattara hankalinsu ga aikin da suke yi na tafiyar da gwamnatinsa, rahoton Punch.

Uwar gidan Osibnajo na taka rawar gani

Amma da take zantawa da wakilin Punch, shugabar mata a jam'iyyar APC, Dr Betta Edu ta bayyana cewa, uwar gidan Osinbajo na taka rawar gani a tawagar kamfen din tallata Tinubu.

A cewarta, bayyanar suna a takardar jerin mambobin majalisar kamfen ba yana nuna irin aiki tukuru da mambobin ke yi bane, domin akwai wadanda ke aikinsu a kasa don ganin nasarar Tinubu da Shettima a zaben 2023.

Kara karanta wannan

Kamfen 2023: Tinubu ya yi magana mai girma game da bashin da ake bin Najeriya

A cewarta:

"Yanzu, uwar gidan mataimakin shugaban kasa, tana taka rawar gani a wannan kamfen. Cewar babu sunanta a jeri ba ya nufin ba ta taka rawar gani a kamfen din bane."

Buhari Ya Kaddamar da Kwamitin Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa Na Jam’iyyar APC

A wani labarin, shugaban kasa Muhammadu Buhari na Najeriya na jagorantar taron kaddamar kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam'iyyar a gidan gwamnati dake Abuja.

Jaridar Punch ta ce ta samo cewa, an tsaurara tsaro a zagayen dakin taron, baki na shan fama wajen shiga cikinsa, ciki har da gwamnoni da manyan baki.

An ga dandazon jama'a a bakin Banquet Hall na gidan gwamnati, ga kuma tulin jami'an tsaron farin kaya (DSS) dake kai komo a kewayen wurin, inji rahoton Vanguard.

Asali: Legit.ng

Online view pixel