Rashin Lafiya Ya Jawo Aka Gaggauta Fita da Atiku Kasar Waje - 'Dan Kwamitin Zaben APC

Rashin Lafiya Ya Jawo Aka Gaggauta Fita da Atiku Kasar Waje - 'Dan Kwamitin Zaben APC

  • Femi Fani-Kayode ya fito yana cewa Atiku Abubakar ya kamu da rashin lafiya ana tsakiyar yakin takara
  • Darektan yada labarai a kwamitin yakin neman zaben Bola Tinubu ya bayyana wannan a shafukansa
  • Fani-Kayode yace an wuce da ‘dan takaran PDP zuwa Birnin Faris, akasin abin da Hadiminsa ya fada

Abuja - Tsohon Ministan tarayya, Femi Fani-Kayode ya yi ikirari Atiku Abubakar mai nemam zama shugaban kasa a jam’iyyar PDP bai da lafiya.

Ana zargin an fita da ‘dan takarar shugabancin kasar na 2023 zuwa ketare domin ya ga Likita, amma hadimin Atiku Abubakar ya musanya hakan.

Cif Femi Fani-Kayode wanda yanzu shi ne Darektan yada labarai a kafar zamani na kwamitin yakin neman zaben Bola Tinubu ya bayyana haka.

Kara karanta wannan

Ku Zabi Tinubu Zai Kare Muradun Arewacin Najeriya, Sanata Abu Ibrahim

A wani bayani da ya yi a shafin Facebook a yammacin Talata, Femi Fani-Kayode yace Atiku Abubakar ya fara rashin lafiya bayan barin Kaduna.

A cewarsa, da aka sauka a filin jirgin saman Abuja sai ya ji ko ina a jikinsa yana yi masa ciwo sosai. Jaridar Daily Post ta kawo labarin nan a yau.

Daga nan aka fita da shi zuwa birnin Faris domin likitoci su duba shi. Babu wata hujja da 'dan siyasar ya bada da za ta tabbatar da labarinsa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Atiku
Atiku Abubakar a jirgin sama Hoto: www.sunnewsonline.com
Asali: UGC

Jawabin Femi Fani-Kayode

"Bayan yawon kamfe da ya yi jiya a Kaduna, Atiku Abubakar ya kamu da mummunan rashin lafiya.
Ya koka da cewa yana jin jiri da matsanancin zafi a kai da kuma duka jikinsa a cikin jirgin sama a kan hanyarsu ta zuwa Abuja.

Kara karanta wannan

Abubuwan da Na Tambayi Peter Obi a Zaman da Nayi da Shi inji Sheikh Ahmad Gumi

Bayan ya sauka a filin tashi da saukar jiragen sama na Abuja, sai ya fadi. Nan take aka wuce da shi zuwa birnin Faris (Faransa).
Saboda ayi rufa-rufa, sai suka dauki hotonsu tare da shi (Atiku) washegari daga birnin Faris, amma ka da ku bari a rude ku.
Akwai matsala tattare da ‘dan takaran PDP na zaben shugaban kasa game da lafiyarsa da ake boyewa ‘Yan Najeriya."

- Femi Fani-Kayode

Independent tace Fani-Kayode ya kare jawabi a Twitter da yi wa 'dan takaran addu'a. A farkon shekarar badi za ayi zaben sabon shugaba a Najeriya.

Atiku yana Najeriya?

Rahoto ya tabbatar da cewa Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma ‘dan takarar shugaban kasar jam’iyyar PDP yayi tafiya zuwa Turai a daren yau.

Ana tsakiyar yawon kamfe, sai rohotanni suka bayyana yadda Atiku ya yi tafiyar domin neman lafiya, duk da Kakakinsa, Paul Ibe ya musanta haka.

Kara karanta wannan

TY Danjuma Zai Gina Sabuwar Jami'ar Kiristoci A Jihar Neja, Gwamna Ya Bada Kyautan Fili Hekta 100

Asali: Legit.ng

Online view pixel