El-Rufai: Dalilin Gwamnonin Arewa Na Goyon Bayan Tinubu Ya Zama Shugaban Kasa

El-Rufai: Dalilin Gwamnonin Arewa Na Goyon Bayan Tinubu Ya Zama Shugaban Kasa

  • Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai ya yi bayanin dalilin Gwamnonin Arewa na bin bayan Asiwaju Bola Tinubu
  • Malam Nasir El-Rufai yace za su marawa Bola Tinubu baya ya zama shugaban kasa saboda hakan ne adalci
  • A cewar Gwamnan, ba daidai ba ne su yarda wani ‘Dan Arewa ya sake yin mulki bayan sun yi shekaru takwas

Kaduna - Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna, ya bayyana abin da ya sa mutanen yankin Arewacin Najeriya za su zabi APC a shekara mai zuwa.

The Nation tace Mai girma Nasir El-Rufai ya yi wannan jawabi a jihar Kaduna, inda yace suna tare da Asiwaju Bola Tinubu a 2023 ne saboda adalci.

Gwamnan yake cewa sun yarda mulki ya koma kudu ne domin ko Ahmadu Bello da Abubakar Tafawa Balewa suna raye a yau, su ma hakan za suyi.

Kara karanta wannan

Ziyarar da Peter Obi Ya Kai wa Dr. Ahmad Gumi ta Jawo Masa Bakin jinin Magoya baya

Malam Nasir El-Rufai yake cewa gwamnonin Arewa ne Magadan Sardaunan Sokoto da Tafawa Balewa, don haka ba za su yarda a hana kudu mulki ba.

A ra’ayin Gwamnan, ba daidai ba ne bayan Muhammadu Buhari ya yi shekaru takwas, a sake samun wani a Arewa ya dare kujerar shugaban kasa.

El-Rufai
Nasir El-Rufai tare da Bola Tinubu Hoto: @officialasiwajubat
Asali: Facebook

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Jawabin Gwamna Nasir El-Rufai

“Lokacin da Gwamnonin APC na Arewa suka yi wani zama a ranar Asabar, suka ce dole mulki ya koma kudu, mun yi haka ne saboda sanin tarihinmu.
Mun tambayi kan mu a matsayin Gwamnonin Arewa, me Ahmadu Bello da Tafawa Balewa za su yi a irin wannan yanayi, me Aminu Kano za iyi?
Mun dauki wannan matsaya a kan wasu da ke hakikancewa bayan shugaba Buhari ya yi shekaru takwas, daga Arewa za a samu wanda zai gaje shi.

Kara karanta wannan

'Yan Arewa mu wayayyu ne: El-Rufai ya tuna yadda Peter Obi ya ci mutuncinsa a 2013 saboda ya je Anambra

Mun ji cewa mu a matsayin gwamnonin Arewa, wannan bai cikin halinmu, ba haka muke ba. Mu mutane ne da aka sani da daraja da kuma adalci.
Idan muka ce za muyi abu, to za muyi, mu cika alkawari, haka muka dauko Bola Tinubu.

An rahoto tsohon Ministan na birnin tarayya yana yi wa Bola Tinubu alkawari mutanen yankin Arewa za su mara masa baya domin ya rike Najeriya.

'Yan takara sun zauna da manyan Arewa

A baya an ji labari Kwamitin hadaka na kungiyoyin Arewa da za iyi zama da ‘yan takarar shugaban kasa ya karyata zargin da wasu ke yi masa na son-kai.

Da yake bayani a shafinsa na Facebook, Hakeem Baba Ahmed ya bayyana cewa Kwamitin hadakan bai da nufin tallata wani 'dan takara ta bayan-fage.

Asali: Legit.ng

Online view pixel